Ghana: 'Yan mata sun rungumi kwallon zari-ruga


Ghana Rugby

A Ghana, kasar da aka kiyasta cewa tana da mutane sama da miliyan 28 a shekarar 2016, ba kowa ne ya san kwallon zari-ruga ba, ko da da sunan wasan na Ingilishi, wato Rugby.

Sai dai masu sha’awar wasan a karkashin jagorancin Hukumar Kwallon Zari-ruga ta Ghana sun dukufa don ganin labarin ya sauya.

“Tun baya da muka rungumi zari-ruga, sai [muka ga ya wajaba] mu kirkiri wani tsari…[wanda] a karkashinsa za mu bunkasa wasan a tsakanin matasa, da mata, kuma a fadin kasar nan”, in ji Shugaban Hukumar, Herbert Mensah.

Wannan yunkuri da kuma burin da suke da shi na samar da ‘yan wasa akalla 1,500 su suka aka daura damarar ganin an koyar da zari-ruga a makarantu 120 nan da shekarar 2020.

Wasan zari-ruga a makarantu

Hakan ne kuma ya kai ga horar da wasan a wata makarantar firamare ta Islamiyya mai suna Al-Walid da ke unguwar Kanda a birnin Accra.

Wakilinmu Muhammad Fahd Adam ya ziyarci makarantar inda ya tarar dalibai mata na atisaye, a filin wasa na makarantar mai jar kasa, galibinsu sanye da hijabi, wasu da takalmi wasu kuma babu ma takalmin a kafarsu.

Mai horar da su, Rafatu Inusa, ma’aikaciya ce a Hukumar Zari-Ruga ta Ghana ta kuma shaida wa BBC cewa: “Muna so a cikin unguwanninmu da makarantunmu kowa ya rungumi rugby, musamman yara mata saboda rugby wasa ne na kowa da kowa.

“Ba [wasa ne da za a ce mai] jiki ba za ta iya ta bugawa ba, ko [a ce] wata guntuwa ce; [ko] kana da jiki, [ko] ba ka da jiki, kowa na da [rawar da zai taka] a wasan rugby.

“A cikin yaran makarantun mun samu wadanda suke shiga kulob-kulob, don su samu damar buga wa tawagar kasa, don haka…mata duka muna son su rungumi wasan rugby”.

A yanzu haka dai akwai kungiyoyin zari-ruga guda 13 a kasar ta Ghana.

Burin Hukumar Zari-Ruga

Burin Hukumar Kwallon Zari-Ruga ta Ghana shi ne samar da kwararrun ‘yan wasa, musamman mata ‘yan kasa da shekara 14, wadanda za su wakilci kasar a duniya.

Ga alama kuma sai sun dauki hanyar cimma wannan buri, don kuwa ‘yan mata da dama a makarantar Alwalid tuni suka shiga buga wannan gasa ka’in da na’in.

A cewar Zainab Abdulrahman, “Na iya [wasan zari-ruga] sosai; ina so na zama kwararriyar ‘yar wasan rugby”.

Amma ba a nan burinta ya tsaya ba, tana kuma “so in gwada ma yayana da kannena”.

“Wasa ne na maza?”

Wasu dai na ganin kwallon zari-ruga wasa ne na maza majiya karfi, musamman saboda yadda ake turereniya da sheka gudu da sauransu..

Amma wadannan ‘yan mata da suka rungumi wasan sun ce ba haka lamarin yake ba.

A cewar Maimuna Muhammad Dawud, “Ni a ganina ba na maza ba ne [su kadai]; har da mata ma za su iya bugawa.

“Shi yasa nake sha’awarsa, kuma ina buga rugby [saboda] idan ‘yan uwana mata suka gani, za su so su ma su buga.”

To ko me ya sa aka zabi makarantar Islamiyya, kuma ta mata, don koyar da wannan wasa na zari-ruga?

Koci Rafatu, wadda ita ma Musulma ce, cewa ta yi wannan ba abin mamaki ba ne, “Saboda [duk da cewa] yaran musulmi [ne], kar ku duba wai addini kaza kaza…ke mace ki sanya hijabinki, ki tabbatar ko ina naki yana rufe, idan yana rufe babu abin da ba za ki iya yi ba.

“Tun da dai ba ku da maza za ku buga ba—mu mata zallanmu ne—ba [wata] mishkila”.

Hukumar Kwallon Zari-Ruga dai ta ce zuwa yanzu a yunkurin tallata wannan wasa sai hamdala.

A cewar Mista Mensah, “Kamar kowanne shiri, za ka samu nasara ne idan akwai wadanda suka jajirce, kuma tabbas ni na jajirce.

A wannan shekara, a karo na farko, mun kaddamar da league na mata wanda aka samu nasarar kammalawa.

“An samu nasara a bangaren yawan kungiyoyin da suka fafata, an kuma yi nasara dangane da irin mutanen da suke buga wasan daga addinai daban-daban da kabilu daban-daban da sauransu.

“An samu gagarumar nasara saboda wasan ya yi armashi, an bi dokoki, an samu karancin raunuka, [kuma] akwai hamasa sosai, saboda haka abin ya burge matuka”.

Ma'aikaciyar rediyo ta haihu yayin gabatar da shiri


Cassiday Proctor holds her baby, Jameson in hospitalHakkin mallakar hoto
@radiocassiday/Instagram

Image caption

Cassiday Proctor’s baby boy has been named Jameson

Wata mai watsa shirye-shiryen rediyo a Amurka ta haihu yayin da take gabatar da shiri.

Cassiday Proctor, mai gabatar da shirin safe na ranakun aiki na mako a wata tashar da ake kira The Arch a birnin St. Louis na Amurka, ta watsa labarin yadda aka yi mata tiyatar cire jaririnta a ranar Talata.

Ms Proctor ta fara jin nakudar haihuwa ne tun a ranar Litinin. Gidan rediyon da take aiki sun hada kai da asibitin da ta haihu kan yadda za a watsa yadda haihuwar ta kasance a rediyo.

Ta gaya wa BBC cewa ba su shirya zuwan jaririn ba saboda ya zo makonni biyu kafin lokacin da ake tsammanin sa.

Ms Proctor ta ce ta ji dadin iya bayar da labarin daya daga mafi abubuwan da suka fi sa ta farin ciki a rayuwarta ga masu sauraronta a rediyo.

Ta ce “haihuwa a lokacin da take gabatar da shiri tamkar, “kari ne a kan abun da ta saba yi a ko wacce rana a gidan rediyonmu, saboda kullum ina ba da labarin dukkan rayuwata ga masu sauraro.”

An sanyawa jaririn suna Jameson, bayan da masu sauraro suka zabi sunan jaririn a cikin wata gasa da aka gabatar a rediyon a watan Janairu.

'Barin malamai su rike bindiga zai magance matsalar harbe-harbe'


Trump ya ce barin malamai su rike bindiga zai kawo karshen matsalar harbe-harbeHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Trump ya ce barin malamai su rike bindiga zai kawo karshen matsalar harbe-harbe

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce a ganinsa abun da ka iya kawo karshen matsalar yawan harbe-harbe a makarantu a Amurka, shi ne horar da malamai su iya amfani da bindigogi.

Ya bayyana hakan ne a wani taro da ba a taba yin irinsa ba a Amurka, inda wadanda su ka tsira a harbe-harben da a ka sha yi a makarantu da iyayen wadanda su ka mutu su ka gana da Shugaban ido da ido.

Taron wani yunkuri ne na jawo hankalin shugabannin siyasa su sauya ra’ayi a kan manufofin amfani da bindiga a kasar.

A taron da a ka watsa a gidajen talabijin, daya daga cikin mahaifan wadanda su ka mutu a wani harbi da a ka yi a wata makaranta, ya nuna bacin ransa ga kalaman Mr Trump. Inda ya bayyana su a matsayin masu tsananin rauni.

Bincike ya nuna magungunan ciwon da ke sa damuwa na aiki


Bincike ya nuna magungunan ciwon da ke sa damuwa na aikiHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Bincike ya nuna magungunan ciwon da ke sa damuwa na aiki

Masana sun gudanar da wani bincike da ya tabo fannoni da dama a jami’ar Oxford wanda ya musanta bayanan da ke nuna cewa magungunan warkar da ciwon tsananin damuwa ba sa tasiri.

Binciken mai zurfi ya nuna cewa ashirin da daya daga cikin magungunan sun taimaka wajen baiwa marassa lafiya sauki.

Masu binciken sun duba sama da gwaje-gwaje dari biyar kuma sun hada da wasu bayani da aka yi a baya da wasu kamfanonin magunguna su ka ki fitarwa.

Sakamakon da a ka wallafa a wata mujallar kiwon lafiya, The Lancet ya nuna cewa magungunan su na tasiri. Haka kuma, kungiyar likitoci masu kula da masu tabin hankali a Birtaniya ta ce binciken zai kawo karshen duk wani rikici.

Rashawa: 'Har yanzu babu sauyi a Nigeria'


Shugaba BuhariHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Najeriya ce kasa ta 148 daga cikin jerin kasashe 180

Sabon rahoton kungiyar Transperancy International da ke yaki da cin hanci da rashawa a duniya ya ce, har yanzu babu wani sauyi da aka samu a Najeriya a kan yaki da matsalar.

A rahoton da kungiyar ta fitar ta ce Najeriya ce kasa ta 148 daga cikin jerin kasashe 180 da kungiyar ta yi nazarin girman matsalar a 2017.

Transparency ta ce Najeriya ta samu maki 27 ne kacal daga cikin maki 100 da ya kamata ace kasa ta tsira daga matsalar rashawa.

Rahoton kungiyar ya ce matsalar ta kara tsanancewa a Najeriya ne idan aka kwatanta da alkalumman shekarar 2016 inda kasar ta samu maki 28. kuma a matsayin kasa ta 136 a duniya.

Daga matsayi na 136 a 2016 a bana Najeriya ta koma ta 148 a cewar rahoton.

Rahoton kuma ya ce a Nahiyar Afrika Najeriya ce ta 32 daga jerin kasashe 52 da Transperency ta yi nazari kan girman matsalar rashawa.

A cewar rahoton na 2017, Najeriya ce ta biyu a kasashen da matsalar ta fi yin kamari a Afirka bayan Botswana.

Kungiyar CISLAC reshen kungiyar Transparency International da ke yaki da rashawa a Najeriya ta ce sakamakon rahoton abin damuwa ne.

A wata sanarwar bayan fitar da rahoton, CISLAC ta ce tun hawan gwamnati mai ci a yanzu da ke da’awar yaki da cin hanci da rashawa, babu wani hukunci da aka yanke kan ‘yan siyasar da aka samu da laifin rashawa.

CISLAC ta ce wannan koma-baya ne a yaki da cin hanci da rashawa, kuma hakan ya tabbatar da girman cin hanci da rashawa musamman rashawa a siyasa da alfarma da azurta dangi.

Kungiyar ta ce duk da akwai dubarun yaki da rashawa gwamnati mai ci ta tsara a 2017 da wasu kudururruka da ta yi alkawali a cikin gida da kasashen waje amma har yanzu ba wani abin azo gani da aka aiwatar.

A cikin sanarwar, CISLAC ta bayar da wasu shawarwari da ta ke ganin idan an bi za a iya shawo kan girman matsalar rashawa a Najeriya.

Shawarwarin sun hada da fadada dubarun yaki da cin hanci da rashawa zuwa karkara tare da hada hannu da kungiyoyin fararen hula domin su sa ido tare da aiwatarwa.

Da kafa kotuna na musamman kan yaki da rashawa tare da nada alkalan da aka tabbatar tsabtatattu ne.

Sannan da karfafawa hukumomin da ke yaki da cin hanci da rashawa da kariya ga masu kwarmato da kuma karfafawa kafofin watsa labaru.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

‘Yan Najeriya sun zabi Buhari don yaki da rashawa

Tun a hawansa kan mulki, shugaba Buhari ya bayyana cewa cin hanci da karbar rashawa ba su da wuri a gwamnatinsa, abin da ya sa wasu ke tunanin zai yi irin ba-sani ba-sabon da ya yi a lokacin yana mulkin soja a shekarar 1984.

Gwamnatin Buhari ta kwato kudade da wasu jami’an gwamnatin da suka gabata suka kwace, sai dai har yanzu babu wanda aka gurfanar a kotu.

Sannan gwamnatin Buhari ta sha musanta zargin cewa ta fi karkatar da yaki da cin hanci da rashawa ga ‘yan adawa, maimakon yakar matsalar da shugaban ya ce ita ce ta hana kasar ci gaba.

A watan Oktoban 2017 ne Buhari ya kori sakataren Gwamnatinsa Babachir Lawal, da kuma shugaban hukumar tattara bayanan sirri ta NIA Ambasada Ayo Oke da aka samu da almundahana.

An fara hada agogon da zai yi aiki shekaru aru-aru


Karafan da masu ziyara ke wanawa masu kama da kacar keke da ke karawa baitirin agogon karfiHakkin mallakar hoto
Eyewire Inc

An fara aikin hada wani agogo da zai aiki a shekaru aru-aru ba tare da bil’adam sun sanya hannu a gyaran shi ba.

Agogon mai shekara 10,000 na Cibiyar Long Now Foundation ne, wata cibiya mai zaman kanta wadda ke rajin tabbatarda dorewar tunanin bil’adama.

Kamfanin Amazon mallakar Jeff Bezos, shi ya samar da agogon, da aka girke shi a kusa da tsaunukan da ke hamadar Texas.

Babu takamaiman lokacin da aka dauka wajen yin agogon, da lokacin da aka girke shi.

Wanda ya kera agogon da hannunsa shi ne Danny Hillis dan Amurka, kuma a shekarar 1995 ne aka wallafa bayanai kan agogon.

A cikin agogon an yi amfani da wata fasaha da ke bai wa agogon damar kadawa ko bugawa sau daya a shekara, da kuma wani hannu da baya motsi sai bayan shekara 100 da kuma wata kara da sai bayan shekara 1,000 ake jin ta.

Haka kuma, agogon ya samu karfin yin aiki ne idan ya na zuko sauye-sauyen yanayin da duniya ke zuwa da su lokaci zuwa lokaci. Kuma wannan ne ke karawa sauran madannan da ke jikin sa karfi.

Sai dai kuma ba ya iya adana makamashi mai karfin da zai sa agogon ya dinga aiki a ko wanne lokaci har sai masu ziyara sun kunna agogon sannan sun dinga tura wata kaca mai kama da tayar keke ta haka ne batirin ya ke kara karfi, kamar yadda cibiyar Long Now Foundation ta bayyana.

A ranar talata ne Bezos, ya wallafa wani hoton bidiyo a shafin twitter kan yadda aikin gyaran agogon ya ke gudana.

Tuni aikin gyaran agogon ya dauki hankalin mashahuran mutane, baya ga mista Bezos na kamfanin Amazon wanda ya bada tallafin dala miliyan 42 don yin gyaran.

Shi ma wani fitaccen mawaki dan Birtaniya Brian Eno, ya kera wani abin kida da zai dinga fitar da sauti daban-daban a kowacce rana, kuma zai dauki shekara 10,000 ya na aiki ba tare da ya tsaya ba.

Cibiyar Long Now Foundation, ta ce masu yawon bude ido suna da damar kai ziyara hamadar Texas domin ganin yadda aikin gyaran agogon ke gudana.

Zakarun Turai: De Gea ya ceci Man United


David de Gea ya kade wani hari da 'yan Sevilla suka kai wa Man UnitedHakkin mallakar hoto
Rex Features

Image caption

Zuwa yanzu a wasa 19 ba a zura wa David de Gea bal a raga ba. Bai taba kaiwa wasa 20 ba da ba a zura masa bal a raga ba a kaka daya a Manchester United

Mai tsaron ragar Manchester United David de Gea ya ceci kungiyar tasa ta yi canjaras ba ci a gidan Sevilla, a wasansu na farko na zagayen kungiyoyi 16 na kofin zakarun Turai, a ranar Larabar nan.

Golan na Spaniya ya rike kade miyagun hare-haren da ‘yan wasan Sevilla Joaquin Correa da Steven N’Zonzi da kuma Luis Muriel suka kai.

United wadda wannan ne wasanta na farko a matakin sili-daya-kwale na gasar ta zarun Turai a cikin shekara hudu, ba ta kai wasu hare-hare masu yawa ba, kamar wanda Lukaku ya barar tun da farko da kuma na Rashford an kusa tashi.

Paul Pogba ya shigo wasan daga baya a minti na 17 lokacin da aka sauya Ander Herrera wanda ya ji rauni.

‘Yan Sevilla da suka kai hare-hare 25 ba su ji dadin wasan ba, saboda yadda De Gea ya hana su ci da kuma barar da damarsu da suka yi.

Manchester United za ta fi jin dadin yadda wasan ya kare, yadda za ta karbi bakuncin karo na biyu a Old Trafford ranar talata 13 ga watan maris, inda suka yi nasara a wasa 15 daga cikin 18 a gidansu

Kofin Europa: Wenger zai hutar da manyan 'yan wasa


Dan wasan Ostersunds Saman Ghoddos (a tsakiyacentre) da Mesut OzilHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Mesut Ozil ba zai buga wasansu na biyu da Ostersunds sabo da rashin lafiya

‘Yan wasan tsakiya na Arsenal Aaron Ramsey da Mesut Ozil ba za su yi wasa na biyu na kofin Turai na Europa matakin kungiyoyi 32, da Ostersunds FK ranar Alhamis.

A karawarsu ta farko a Sweden kociyan kungiyar Arsene Wenger ya tafi da kusan cikakkiyar tawagar ‘yan wasansa, inda suka ci wasan 3-0, amma yanzu zai yi amfani da wasu daga cikin matasan ‘yan wasansa a Emirates.

Wenger ya ce, Ozil mai shekara 29 ba shi da lafiya, haka shi ma Ramsey yana murmurewa ne daga ciwon matse-matsi, amma ya ce hakan ba yana nufin zai yi wasarere ba ne da wasan.

Amma kociyan ya ce da Ozil kalau yake to da lalle zai sa shi, dangane da Ramsey kuwa, ya ce, duk da cewa dan Wales din mai shekara 27 ba zai yi wasan na Alhamis ba, ba zai kawar da yuwuwar sa shi a wasan karshe na ranar Lahadi na cin kofin Carabao ba.

Arsenal tana ta shida ne a teburin Premier, maki takwas tsakaninta da ta hudu Chelsea, kuma tana bukatar ta kammala kakar a cikin kungiyoyi hudu na gaba, ko kuma ta ci kofin Europa kafin ta samu damar shiga gasar zakarun Turai ta gaba.

Firmino ya kauce wa hukunci a rikicinsa da Holgate


Mason Holgate na ture FirminoHakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

‘Yan wasan sun yi sa-in-sa ne bayan da Mason Holgate ya tura Firmino kan allunan talla cikin ‘yan kallo

Dan wasan gaba na Liverpool Roberto Firmino ba zai fuskanci matakin ladabtarwa ba daga hukumar kwallon kafa ta Ingila bayan rigimar da suka yi da dan Mason Holgate na Everton a wasan Kofin FA a Anfield a watan Janairu.

Shi dai Holgate ya yi zargin cewa Firmino ya yi masa kalamai na wariya a lokacin sa-in-sar.

Bayan binciken da ta gudanar, hukumar kwallon ta Ingila, FA, ta ce babu isasshiyar shedar da za a tuhumi dan wasan na Brazil.

Firmino, mai shekara 26, ya amince cewa ya gaya wa Holgate, mai shekara 21, bakar magana a cikin harshen Portugal, amma ya musanta yin amfani da kalaman wariya.

Firmino ya ce a matsayinsa na mutumin da ya gamu da cin mutunci na wariyar launin fata a rayuwarsa, ya san yadda abin yake da zafi.

Ya kara da cewa yana so ya tabbatar wa duniya cewa, domin kawar da duk wani shakku, bai furta wannan kalma ba ko wata makamanciyar wadda aka zarge shi da yi ba wadda kuma kafafen watsa labarai suka ruwaito cewa ya fada.

Hukumar, FA, ta tattara bayanai daga ‘yan wasa 12 da jami’ai daga kungiyoyin biyu da alkalin wasa Bobby Madley da kuma mataimakin alkalin wasa na hudu.

Dukkanninsu ba wanda ya ji kalaman wariyar launin fatar da Mason Holgate ya yi zargin Firmino ya furta.

Ce-ce-ku-cen da suka yi a lokacin wasan da Liverpool ta yi nasara da ci 2-1, ya fara ne lokacin da Holgate ya tura Firmino kan allunan talla, cikin ‘yan kallo, sannan kuma aka ga dan wasan na Everton ya harzuka bayan sun yi musayar kalamai

Sojoji sun kwato ‘yan matan da BH ta sace a Yobe


DapchiHakkin mallakar hoto
GGSS

Sojojin Najeriya sun ceto ‘yan matan makarantar sakandaren garin Dapchi da ke jihar Yobe a arewa maso gabashin Najeriya da Boko Haram ta yi awon gaba da su.

Kakakin gwamnan jihar Yobe Abdullahi Bego ya tabbatarwa BBC cewa sojojin Najeriya sun bi ‘yan Boko Haram tare da kwato gaba dayan matan 51.

Ya ce yanzu haka ‘Yan matan suna hannun sojojin da suka kwato su, kuma nan gaba gwamnatin Yobe za ta yi karin bayani.

Serena Williams: Na kusa mutuwa lokacin haihuwa


Serena WilliamsHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Serena Williams ce ‘yar wasan tennis da ta fi samun nasara a wannan zamanin, inda ta ci kofunan manyan gasa 23

Tsohuwar gwana lamba daya a duniya ta wasan tennis Serena Williams ta ce kiris da ta yi sallama da duniya a lokacin haihuwar ‘yarta Alexis Olympia Ohanian Jr a watan Satumba.

Ba’amurkiyar mai shekara 36, ta dawo fagen gasar kwallon tennis din ne a farkon watan nan na Fabrairu, a lokacin da ta hadu da yayarta Venus Williams suka wakilci Amurka a gasar kofin duniya na Fed Cup.

Sai dai gwanar wadda ta dauki kofin manyar gasar tennis 23 a wata kasida da ta rubuta wa CNN ta bayyana cewa, haihuwar da ta yi ta jawo mata matsaloli na lafiya. Ta ce ta ma yi sa’a da ta tsira da ranta.

Serena ta ce an yi mata tiyata ne aka cire mata ‘yar bayan da bugun zuciyarta ya ragu kwarai a lokacin nakudar,

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Serena na kallon wani wasa na gasar Fed Cup a farkon watan nan tare da ‘yarta Alexis Olympia Ohanian Jr

Sannan kuma ta ce abin da ya biyo baya sa’a 24 bayan haihuwar, kwanaki shida ne na rashin tabbas, kafa daya a duniya daya kuma a barzahu.

Bayan haihuwar sai da ta shafe mako shida a gadon jinya

FA ba za ta hukunta Aguero kan fada da dan kallo ba


'Yan kallo sun mamaye fili bayan wasan Wigan da Man CityHakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Sergio Aguero ya ce mutumin da ya yi sa-in-sa da shi ya tofar masa yawu ne kuma ya zage shi

Hukumar kwallon kafa ta Ingila, ta ce ba za ta hukunta dan wasan gaba na Manchester City Sergio Aguero ba, a kan sa-in-sa da ya yi da wani dan kallo bayan an tashi daga wasan da Wigan ta fitar da su da ci 1-0, a gasar cin kofin FA ranar Litinin.

A wani hoton talabijin an ga Aguero yana ture wani dan kallo wanda kuma daga baya ya ce mutumin ne ya tofar masa yawu da kuma zaginsa.

Hukumar ta FA ta tuhumi dukkanin kungiyoyin biyu da laifin kasa tsawatar wa ‘yan wasansu bayan da alkalin wasa ya kori Fabian Delph na Manchester City.

Jan katin da alkalin wasan ya ba wa Delph a kashin farko na wasan ya jawo ce-ce-ku-ce tsakanin kociyan City Pep Guardiola da takwaransa na Wigan Paul Cook a lokacin da suka kama hanya ta zuwa hutun rabin lokaci, amma hukumar ta FA ta ce ba wani abu na saba doka da ya faru a tsakaninsu.

Kungiyoyin suna da wa’adin zuwa karfe bakwai na yamma agogon Najeriya da Nijar ranar Juma’a su bayar da bahasi.

Sannan kuma an bukaci Wigan da Man City din su gabatar wa hukumar abin da suka sani game da kutsen da ‘yan kallo suka yi zuwa cikin fili bayan an tashi daga wasan.

Kacici-kacicin ranar harshen uwa ta duniya: Shin kun kware a harshen Hausa?


An ware 21 ga watan Fabrairu na ko wacce shekara a matsayin ranar harshen uwa na duniya.

Majalisar Dinkin Duniya ce ta kebe ranar don habaka harsunan duniya da raya al’adu a tsakanin al’umma. Shin wane tasiri sarrafa harshe fiye da guda kan yi a kan harshen uwa?

Taken bikin na bana shi ne: “Ranar masu iya sarrafa fiye da harshe guda.”

Ga wannan kacici-kacicin ku latsa ku yi don sanin ko kun kware a harshen Hausa ko da sauran ku.Aika sakamakonku

Za mu ba wa Barcelona mamaki – Antonio Conte


Antonio ConteHakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Antonio Conte ya ce za su ba wa Barcelona mamaki a Nou Camp, a wasansu na biyu na zakarun Turai

Kociyan Chelsea Antonio Conte ya ce za su yi kokarin yin wani abin mamaki ta hanyar fitar da Barcelona daga gasar kofin zakarun Turai bayan kunnen doki, 1-1 da suka tashi a karon farko ranar Talata a Stamford Bridge.

Conte ya ce suna dab da kammala wasa yadda ya kamata, daidai wa daida, sai suka gamu da sammatsin yin kuskure daya, kawai sai kuma abin takaici labari ya sha bamban.

Kociyan dan Italiya ya ce, sun yi kuskure daya, wanda kuma sun san cewa idan kana karawa da ‘yan wasa irin su Messi da Iniesta da Suarez, muddin ka yi kuskure to za ka illar hakan.

Willian ne ya fara ci wa Chelsea kafin daga bisani ana minti 15 a tashi Lionel Messi ya farke wa Barcelona, aka tashi kunnen doki 1-1.

Barcelona wadda ke jagorantar teburin La Liga da tazarar maki bakwai, ba kasafai ta kai wasu hare-hare masu hadari ba, kafin ta farke.

A ranar Laraba 14 ga watan Maris za su yi karo na biyu na wasan a gidan Barcelona, Nou Camp.

Chelsea ta yi wasanta na karshe a can a kakar 2011-12, kuma duk da alkalin wasa ya kori John Terry a kashin farko na wasan, sun yi canjaras 2-2, inda suka fitar da Barcelona da jumullar kwallo 3-2, a wasan na kusa da karshe.

Daga nan ne kuma Chelsea ta samu nasarar doke Bayern Munich a wasan karshe da bugun fanareti ta dauki kofin.

Za mu daure Alexis Sanchez – kociyan Sevilla


Alexis Sanchez a Manchester UnitedHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Alexis Sanchez ya koma Manchester United daga Arsenal a watan Janairu a wata musaya da Henrikh Mkhitaryan

Kociyan Sevilla Vincenzo Montella ya yi barkwancin cewa kila sai sun daure Alexis Sanchez domin ganin dan wasan na gaba na Manchester United bai yi musu illa ba a karawar zakarun Turai, matakin kungiyoyi 16, da za su yi Larabar nan.

Sanchez mai shekara 29 ya ci bal sau daya ne kawai a wasa biyar da ya yi tun lokacin da ya koma Manchester United a watan Janairu.

Da kociyan yake magana a kan tsohon dan wasan na kungiyar Udinese da Barcelona da kuma Arsenal, Montella ya kara da cewa :” Na san shi sosai tun lokacin da yake wasa a Italiya.”

Ya ce ya gyaru sosai, kuma yana ganin Manchester United tana da dan gaba mai gudun tsiya, wanda kila sai sun sa kwado sun kulle shi ko kuma su sa igiya su daure shi.

Wannan shi ne karon farko da United ta kai matakin sili-daya-kwale a gasar ta zakarun Turai tun 2014, yayin da ita kuwa Sevilla ba ta taba kaiwa wasan dab da na kusa da karshe ba, bayan da Leicester ta doke ta a bara.

Wasan da za a yi a filin Estadio Ramon Sanchez Pizjuan shi ne na biyu da kociyan dan Italiya zai taba jagoranta a gasar cin kofin zarun Turai.

Shi kuwa takwaransa na United Jose Mourinho ya jagoranci wasa 139 a gasar, kuma ya ci kofin sau biyu.

An hallaka 'yan sanda 5 da soja daya a Afirka Ta Kudu


'Yan sanda a bakin aikiHakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Maharan sun yi awon gaba da bindigogi 10 da motar ‘yan sanda

‘Yan sanda biyar da wani soja daya sun rasa rayukansu, a wani samame da suka kai a gabashin birnin Cape Town na kasar Afirka ta Kudun.

A wata sanarwa da kamfanin dillancin labaran kasar ya rawaito ya ce, ‘yan sanda uku sun mutu ne nan take.

Yayin da shi kuma sojan ya rasa ransa ne a lokacin da maharan suke tserewa sun kuma yi garkuwa da jami’an tsaro uku.

Daga bisani aka tsinci gawarsu a bakin hanya, tafiyar kilomita shida tsakanin wurin da ofishin ‘yan sandan.

Sanarwar da gwamnati ta fitar ta tabbatar da cewa maharan ne suka harbe jami’an tsaron sun kware a harbi.

Wasu gungun ‘yan fashi dauke da makamai da ba a san ko su waye ba, su ne suka bude wuta da sanyin safiyar ranar Laraba a ofishin ‘yan sandan.

Kawo yanzu ‘yan sandan ba su san dalilin da ya sa barayin suka kawo harin ba. Sai dai rahotanni sun ce barayin sun kai hari wani injin ba da kudi na wani banki wato ATM tare da kwashe kudin ciki.

Da suka kawo hari ofishin ‘yan sandan sun yi awon gaba da manyan bindigogi 10 da motar ‘yan sanda daya.

Kwamishinan ‘yan sandan Afirka ta Kudu Gen Khehla John Sitole, ya sha alwashin zakulo duk inda maharan suka shiga don su fuskanci shari’a, ya kara da cewa: ”ya na matukar bakin ciki kan abin da ya faru, da alhinin mutuwar ‘yan sandan da soji guda.”

Tuni ‘yan kasar suka fara tofa albarkacin bakinsu ta shafukan sada zumunta da muhawara.

Wani abokin iyalan daya daga cikin mamatan, ya wallafa shafinsa na facebook cewa: ”Kai hari a ofishin jami’an tsaro barazana ce ga tsaron kasa.”

Ya kara da cewa a halin da ake ciki mutane na zaman dar-dar na rashin sanin halin da za su samu kansu a ciki. Saboda idan har za a kai hari ofishin ‘yan sanda a kuma hallaka ‘yan sanda, ko wanne dan kasa ka iya samun kansa a irin halin.

Wakilin BBC a kasar Afirka ta Kudu Milton Nkosi, ya ce gabannin kai harin an gudanar da wani bincike da ya gano an samu raguwa matuka ta kisan ‘yan sanda da kashi 52 cikin 100 tun bayan kawo karshen mulkin wariyar launin fata a shekarar 1994.

An kama wani dauke da zinarin sama da N360m a Kenya


ZinariHakkin mallakar hoto
Getty Images

Jami’an tsaron Kenya sun kame wani dan Tanzania da zinarin da darajarsa ta kai dala miliyan daya, kwatankwachin sama da naira miliyan 360.

An kama mutumin ne mai shekara 45 a tashar jirgin sama ta Jomo Kenyatta a Nairobi, a lokacin da yake kokarin shiga jirgi zuwa Dubai a ranar Juma’a.

Nauyin zinarin da mutumin ke dauke da shi ya kai kilo 32.

Rahotanni daga Kenya sun ce jami’an haraji ne suka kama shi, bayan an tsegunta mu su labari game da mutumin da ke dauke da zinarin.

Yanzu zinarin na hannun jami’an kwastam na Kenya a yayin da ‘yan sanda ke ci gaba da gudanar da bincike.

'Ba a ji duriyar 'yan makarantar Dapchi 90 ba'


GGSS DapchiHakkin mallakar hoto
GGSS Dapchi

Gwamnatin jihar Yobe da ke arewacin Najeriya ta tabbatar da cewa har yanzu babu tabbas din inda wadansu ‘yan mata da aka kai hari a makarantarsu da ke garin Dapchi su ke.

Wadanda suka shaida lamarin sun ce wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne suka kai hari makarantar cikin motoci a kalla 12, suka kuma yi ta harbe-harbe da tayar da ababe masu fashewa, a ranar Lahadi da yamma.

Yayin da suka kusanci makarantar, dalibai da malamai sun gudu zuwa cikin daji da ke kewaye wurin, amma har yanzu ba a ga kusan ‘yan mata 90 ba.

Mutanen da ke zaune a kusa da makarantar sun shaidawa BBC cewa an gano rabin mutanen da suka bace, wadanda suka buya a kauyuka da ke kewaye da garin.

Amma wasu mazauna kauyukan da ke kewaye da garin sun kira BBC a waya inda suka ce sun ga wucewar mayakan dauke da ‘yan mata a motocin nasu.

Sai dai hukumomi ba su tabbatar da cewa ko mayakan Boko Haram din ne suka sace su ba.

Sun kuma ce suna kokarin gano sauran ‘yan matan, ta hanyar duba dazuzzukan da ke kewaye da garin.

Wani malami na makarantar, wanda mayakan suka nemi ya ba su hanya su shiga ginin makarantar ya shaida wa BBC cewa mayakan sun je neman abinci ne.

Malamin ya ce ya tabbatar mayakan ba su je makarantar don neman dalibai ba sai don satar abinci da kayayyakin bukatu.

Ana kwatanta wannan lamari da sace ‘yan matan makarantar Chibok fiye da 200 da mayakan suka yi a shekarar 2014.

Sai dai duk da cewa an gano fiye da rabin ‘yan matan Chibok, har yanzu akwai kusan 100 a hannun mayakan.

Mutumin da ke hawa wani kololuwar tsauni don zuwa coci


Ku latsa alamar hoton da ke sama don kallon bidiyon:

A ko wacce rana wani limamin coci a kasar Habasha, yana yin tafiyar mita 250 a tsaunin da ke arewacin kasar don yin nazarin littafan addini da kuma addu’a.

Kamar yadda za ku gani a wannan hoton bidiyon da Charlie Northcott, Kalkidan Yibeltal da kuma Berihu Lilay suka aiko mana.

Nigeria: Da gaske Yusuf Buhari ya mutu?


Yusuf Buhari ya yi hadarin ne a ranar Kirsimeti a AbujaHakkin mallakar hoto
TWITTER/YUSUF BUHARI

Image caption

Yusuf Buhari ya yi hadarin ne a ranar Kirsimeti a Abuja

Fadar shugaban Najeriya ta karyata labarin da ke cewa dan shugaban kasar Yusuf Buhari ya rasu.

“Yusuf Buhari yana samun sauki a asibitin da yake jinya a kasar Jamus kuma likitoci suna sake duba kansa da ya bugu da kuma kafarsa,” in ji mai taimakawa Shugaba Muhammadu Buhari kan shafukan zumunta, Malam Bashir Ahmad, a hirarsa da BBC.

Wasu shafukan intanet ne suka wallafa labarin da ke cewa dan gidan shugaban kasar ya rasu a ranar Talata da yamma.

Sai dai Malam Bashir ya ce labarin ba shi da kanshin gaskiya, yana mai cewa “ko jiya [Talata] na yi magana da ‘yar uwarsa da ke jinyarsa a asibitin Jamus kuma ta shaida min cewa yana samun sauki sosai.”

Sai dai tun bayan da aka tafi da shi Jamus ba a sake jin wani abu na labarin halin da yake ciki ba daga bakunan wadanda ke da kusanci da fadar shugaban, ko da kuwa a kafafen sada zumunta ne.

Kakakin na shugaban kasa bai fadi ranar da Yusuf Buhari zai koma Najeriya ba.

A farkon watan Janairu ne aka sallami dan Shugaban kasar daga wani asibitin Abuja bayan hadarin da ya yi a watan Disamba.

Wata sanarwa da mai bai wa shugaban kasar shawara kan harkokin watsa labarai Garba Shehu ya fitar, ta ce lamarin ya faru ne a unguwar Gwarimpa da ke birnin da daren ranar Kirstimeti.

A cewar Garba Shehu, “Ya karye a kafa sannan ya ji rauni a kansa sakamakon hatsarin. Kazalika an yi masa tiyata a wani asibiti da ke Abuja amma yanzu yana samun sauki”.

‘Ya’yan masu hannu da shuni kan yi wasan tseren babura akai-akai a wani yanki na kwaryar birnin Abuja, lamarin da ake gani na cike da hatsari.

A shekarun baya, hukumar birnin tarayyar ta haramta yin irin wannan tsere bayan wasu rahotanni da aka samu na tukin ganganci da masu tseren ke yi.

Hakkin mallakar hoto
Facebook/Presidency

Image caption

Yusuf Buhari ya yi hadarin ne a ranar Kirsimeti a Abuja

Trump zai hana amfani da na'urorin karawa bindiga karfin aiki


Na'urar na baiwa bindiga damar yin harbi mai yawa cikin karamin lokaciHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Na’urar na baiwa bindiga damar yin harbi mai yawa cikin karamin lokaci

Shugaba Donald Trump ya yi alkawarin daukar matakan kawar da na’urori da ke baiwa bindigogi damar yin jerin harbe-harbe a cikin kankanin lokaci.

An bai wa Jami’ai a hukumar shari’a izinin kafa dokar da za ta haramta amfani da na’urorin wadanda a ka yi amfani da su wajen hallaka mutum 58 a Las Vegas a watan Oktobar bara.

A baya an sha yin muhawara kan ko hukumomin gwamnati na da damar haramta amfani da wannan na’ura. Amma a yanzu Shugaba Trump ya ba su izinin yin hakan.

Mr Trump dai ya fuskanci matsin lamba tun bayan da a ka yi harbi a wata makaranta a Florida a makon jiya.

Ya kuma nuna cewa zai goyi bayan sabbin ka’idojin kididdige wadanda za su mallaki bindigogi nan gaba.

Sarauniyar Ingila ta halarci bikin nuna kayan kawa


Sarauniyar Ingila ta halarci bikin nuna kayan kawaHakkin mallakar hoto
PA

Image caption

Sarauniyar Ingila ta halarci bikin nuna kayan kawa

Sarauniyar Ingila Elizabeth ta biyu ta halarci taron bikin nuna kayan kawa a Landan a karo na farko tun hawanta mulki shekaru sittin da su ka gabata.

Sarauniyar ta zauna a sahun gaba a taron, a gefen babbar editar mujallar Vogue, Anna Wintour.

Sarauniya Elizabeth ta bai wa wani mai tsara dinkunan kayan kawa Richard Quinn lambar yabo ta Queen Elizabeth II Award for British Design a wajen taron.

Ta kuma bayyana shi a matsayin wani babban jigo a fannin kayan kawa a Birtaniya.

Kacici-kacici: Wanne tauraron fim din Black Panther ku ke wakilta?


Fim din gwarzaye na kamfanin Marvel na farko kenan taurarinsa suka kasance bakaken fata, ya kuma yi matukar farin jini har ana sa ran zai kafa tarihi sosai.

Ana kuma yabon fim din da kasancewa wanda ya nuna al’adun bakaken fata a Hollywood.

Manhajar na’urarka ba za ta iya nuna bayanan nan ba.


Kacici-kacici kan fim din Black Panther


Kacici-kacici kan fim din Black Panther


Wa ye kai a cikin taurarin?

Nemi wanda ka dace da shi a sabon fim gwaraza


Wadanda suka yi aikin

Shiryawa, Yemisi Adegoke, Tsarawa, Olaniyi Adebimpe da Olawale Malomo.

Hakkin mallakar hotuna

Marvel Studios, Getty Images

Zakarun Turai: Barcelona ta rike Chelsea 1-1, Bayern ta casa Besiktas 5-0


Lionel Messi lokacin da ya farke wa BarcelonaHakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Bal din da Lionel Messi ya ci ita ce ta 28 a kakar nan, kuma ta farko a wasa shida na karshe

Lionel Messi ya ci kwallon da ya farke wa Barcelona ta hana Chelsea samun muhimmiyar galaba a wasansu na farko na matakin kungiyoyi 16 na kofin zakarun Turai a Stamford Bridge.

Willian wanda sau biyu yana yi wa Barcelona kararrawa, yana sharara bal tana dokan tirken raga, shi ne ya yi dacen cin bakin a minti na 62.

Sai dai kuma nasarar ta Chelsea ta yi karko ne na minti 13 kawai, kafin Andreas Christensen ya yi kuskuren bayar da wata bal, wadda takwaransa na Barcelonan and Andres Iniesta ya tsine ta, kuma bai yi wata-wata ba ya nemi Messi, wanda ya daddage ya kwarara wa Thibaut Courtois, ta kwana a raga.

Kungiyoyin za su yi karawa ta biyu ne a ranar Laraba 14 ga watan Maris a gidan Barcelona, wadda take da dama fiye da Chelsea saboda kwallon da ta zura musu a gida.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Bayern ta mamaye wasan da sama da kashi 68 cikin dari a kan Besiktas

A daya wasan na zakarun Turai da aka yi a daren na Talata zakarun Jamus, Bayern Munich ta caskara Besiktas 5-0, bayan da alkalin wasa ya kori dan wasan kungiyar ta Turkiyya, Domagoj Vida a minti na 16.

Jirgin Dana ya abka cikin daji bayan ya sauka a fatakwal


Jirgin Dana ya taba kashe mutane sama da 150 a LagosHakkin mallakar hoto
Sahara Reporters

Image caption

Jirgin Dana ya taba kashe mutane sama da 150 a Lagos

Daya daga cikin jiragen kamfanin Dana a Najeriya ya abka cikin daji a yayin da yake kokarin tsayawa bayan ya sauka a garin Fatakwal.

Jirgin na Dana wanda ya fito daga Abuja ya kamata jirgin ya tsaya bayan ya sauka, amma rahotanni sun ce sai ya zarce iyakar titin sauka har ya abka cikin daji.

Daga cikin dajin na tashar jirgin saman a Fatakwal aka kwashe fasinjan da ke cikin jirgin.

Rahotanni sun ce babu wanda ya ji rauni daga cikin fasinjan jirgin.

Jirgin Kamfanin Dana ya taba yin hatsari a Lagos inda ya kashe mutane sama da 150 a shekarar 2012.

An tuhumi West Ham kan amfani da abubuwan kara kuzari


Filin wasa na West HamHakkin mallakar hoto
Others

Image caption

Ana tuhumar West Ham da laifin saba ka’idar da ta shafi dokar amfani da abubuwan kara kuzari

Hukumar kwallon kafa ta Ingila FA, ta tuhumi kungiyar West Ham da laifin da ke da nasaba da saba ka’idar amfani da abubuwan kara kuzari.

An zargi kungiyar ta gasar Premier ne wadda a karo uku cikin wata 12 ta kasa tabbatar da ganin bayanan da suka danganci inda ‘yan wasanta suke, daidai suke, ba wani sabani ko kuskure.

Kungiyar tana da wa’adin nan da ranar 27 ga watan nan na Fabrairu ta bayar da bahasi kan tuhumar.

Wani mai magana da yawun kungiyar ta West Ham a wata sanarwa ya ce, matsalar ta shafi harkokin gudawar ne kawai, amma ba wani dan wasa ba.

Hukumar kwallon kafar ta Ingila ba ta fito fili ta bayyana takamaimai irin ka’idar da kungiyar ta saba ba.

A ka’ida dai kowa ce kungiya kan gabatarwa da hukumar kwallon ta Ingila bayanan inda ‘yan wasanta suke, domin ta kan kai ziyarar bazata, inda ake yi wa ‘yan wasa gwaji na abubuwan kara kuzari da aka haramta amfani da su a wasa.

Antonio Conte ya kasa barci saboda Barcelona


Kociyan Chelsea Antonio ConteHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Chelsea ta ci wasa hudu ne kawai daga cikin 12 da ta yi a baya bayan nan

Kociyan Chelsea Antonio Conte ya ce ya kasa barci a ‘yan kwanakin nan saboda wasan da kungiyarsa za ta yi na matakin kungiyoyi 16 na zakarun Turai da Barcelona a Stamford Bridge.

Ya ce a kwanakin nan bayan wasan da aka fitar da su daga gasar kofin FA, tun daga wannan lokacin ya kasa samun barci da kyau.

Conte ya ce ya samu kansa cikin wannan yanayi ne saboda zai fuskanci kungiyar da take daya daga cikin fitattun gwanaye na duniya, kuma wadanda ma ake kallon za su dauki kofin na Turai.

Barcelona na kan hanyarta ta cin kofuna uku ne a bana kuma kawo yanzu ba a doke su ba a gasar La Liga, wadda suke kan gaba da tazarar maki bakwai.

Sai dai kuma kociyan dan Italiya ya ce, a daya bangaren suna murna da hakan saboda wata dama ce a wurinsu ta su tashi tsaye su nuna iyawarsu a kan wannan babbar kungiya, kuma su nuna matsayinsu.

Chelsea dai ta ci hudu ne kawai daga cikin wasanninta 12 da ta yi a karshen nan.

Kungiyar ta yi rashin nasara a hannun Arsenal a wasansu na kusa da karshe na cin kofin Carabao (EFL) a watan Janairu, sannan kuma ta sha kashi a gasar Premier a hannun Bournemouth da Watford.

Sai dai kuma kungiyar ta fara farfadowa inda ta yi nasara a kan West Brom a gasar Premier ranar 12 ga watan Fabrairu, ta kuma biyo baya da doke Hull City, a wasan cin kofin FA zagaye na biyar ranar Juma’a.

Ana dai ta muhawara a kan makomar Antonio Conte a kungiyar ta Chelsea a bana, kuma bayan wasan nasu da Barcelona zai fuskanci wata babbar karawar da Manchester United a wasan Premier ranar Lahadi.

'Satar abinci ce ta kai 'yan Boko Haram makarantar 'yan mata a Yobe'


abinciHakkin mallakar hoto
Getty Images

Ana ci gaba da samun rahotannin kan harin da wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne suka kai wata makarantar sakandaren ‘yan mata da ke garin Dapchi, a jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Wani malami na makarantar, wanda mayakan suka nemi ya ba su hanya su shiga ginin makarantar ya shaida wa BBC cewa mayakan sun je neman abinci ne.

Malamin ya ce ya tabbatar mayakan ba su je makarantar don neman dalibai ba sai don satar abinci da kayayyakin bukatu.

Mayakan dai sun yi nasarar tafiya da kayan abinci bayan sun shafe sa’a uku a cikin makarantar.

Babu dai wanda ya ji rauni a harin da aka kai din, kuma tuni aka rufe makarantar tun bayan faruwar lamarin a ranar Litinin.

A yanzu haka dakarun soji ne suke zagaye da makarantar.

Ganau sun ce mayakan sun shiga garin ne suna harbe-harbe da kuma tayar da ababen fashewa da misalin karfe 6 na yamma.

A lokacin da suka isa mashigar makarantar, sai mafi yawan dalibai da malaman suka gudu cikin daji suka buya.

Malamin ya kara da cewa har zuwa lokacin da ake rubuta labarin nan wasu daliban ba su koma ba, amma bai yarda cewa mayakan Boko Haram din ne suka dauke su ba.

Rundunar sojin Najeriya dai na ci gaba da dannawa cikin dajin Sambisa inda nan ce maboyar ‘yan Boko Haram, kuma ta ce tana samun nasara sosai.

BBC ta samu labarin cewa saura kiris sojojin Nigeria su kama jagoran kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau a wani farmaki da aka dakatar da su.

Bayan kwana 10 da faruwar hakan kuma sai suka shiga sansani da aka yi amanna can Shekau ke boye, amma sai suka samu ya tsere.

A wani faifen bidiyo da BBC ta samu daga hannun wasu da ke fafutika tare da sojojin Najeriyar, an ga yadda sojojin ke kai wa da komowa a wasu sansanoni na wucin gadi a dajin Sambisa.

Bola ta rufto ta kashe yara 17 a Mozambique


Mutane dai sun taru dan taimakawa wadanda bolar ta fado kansu, da kayayyakinsu da bolar ta rufeHakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Hukumomin yankin sun gargadi mazauna kusa da bolar su yi taka tsan-tsan

A kalla mutane 17 aka tabbatar da mutuwarsu, ciki har da kananan yara a birnin Maputo, wasu da dama kuma suka ji mummunan rauni a lokacin da bola ta rufto kansu.

Jami’ai a yankin sun ce wata bola da ta yi torokon mita 15 ita ce ta rufto, a lokacin da ake tafka ruwan sama da tsakar ranar Talata.

Wurin da bolar ta ke dai, matsugunin daruruwan matalauta da suka gina dakunansu da langa-langa ko katako ne.

Bolar ta bi ta kan wasu gidaje biyar da ke gefenta.

Ma’aikatan ceto na ci gaba da tona bolar ko za su sake samun wasu mutane ko kayan da lamarin ya rutsa da su.

Mai magana da yawun hukumar agajin gaggawa, Leonilde Pelembe, ya yi gargadin a yi taka tsantsan don ta yiwu akwai karin mutanen da bolar ta danne.

”Bayanan da muka samu daga hukumomin yankin sun ce mutanen da suke zaune a wurin bolar sun fi wadanda aka ba mu bayanin sun mutu, ” in ji Mista Pelembe.

Gundumar Hulene da ke Maputo, daya ne daga cikin wuraren da ba a damu da su ba a birnin. Yawancin mazauna gundumar su na samawa kansu matsuguni ne ko dai a can saman bolar ko kuma a gefe, ciki kuwa har da kananan yara.

Bolar ba wai ta na zame musu hanyar samun abinci ba ne kadai, har ta kan zama sanadin samun kudaden shiga kamar yadda wakilin BBC Jose Tembe ya bayyana.

Hadarin da ake jiran ya faru?

Sharhi daga wakilin BBC na Afirka a birnin Moputa Jose Tembe

Wakilin BBC ya ce tun ya na karami ya taso ya ga bolar a wurin, a shekarar 1980. Zai iya tuna lokacin da aka fara gine-gine a wurin.

Lokuta da dama, hukumomin yankin sun yi ta kokarin korar mutane tare da kwashe bolar. Duk lokacin da damuna ta kama, jami’ai na zuwa tare da bai wa mutanen wurin wasu filaye don su bar inda suke.

Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Masu aikin ceto na kwashe bolar dan sake neman wadanda suka makale

Da zarar damuna ta wuce, mutanen sai su sake dawowa wurin bolar.

Nan ne wurin da ya fi mu su kusa da birni, da samun kayan ‘Jari bola’ dan saidawa, wasu lokutan kuma sukan samu kayan abinci na gwangwani da manyan shaguna suke zubarwa dan lokacinsu ya wuce. Ko dai dan su ci, ko kuma saidawa.

Gwamnati ta sha daukar alkawarin za ta rufe wurin bolar baki daya, amma har yanzu hakan ba ta samu ba.

Rashin rufe wurin ya sanya, har yanzu mutane su na zaune a yankin.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa, hukumomin sun ce a baya sun ce mazauna yankin su fice daga nan saboda gine-ginen da suka yi ba bisa ka’aida ba ne amma shiru babu alamun za su tashi.

Wani mazaunin yankin da dansa ya ji rauni sakamakon zaftarowar bolar, ya shaidawa BBC cewa ba shi da wurin da zai koma idan ya bar unguwar, idan gwamnati ta bukaci su koma wani wuri da suka tallafa musu ginanne babu abin da zai sa ya ci gaba da zama a wurin mai cike da hadari.

An sheka ruwan sama kamar da bakin kwarya a brnin Maputo tun daga ranar Lahadi da ta wuce, hakan ya janyo ambaliyar ruwa da lalata gidajen jama’a.

A yankunan da matalauta suka fi yawa a birnin Maputo, wasu mutane na zaune ne a filayen da ba nasu ba, da fatan za su samu aikin yi kafin su tashi.

Haka kuma gine-gine a gefen bolar na cike da hadari saboda kamuwa da cututtuka kamar amai da gudawa.

Sergio Aguero ya yi fada da mai goyon bayan Wigan


Magoya bayan Wigan a cikin filiHakkin mallakar hoto
Others

Image caption

‘Yan sanda sun ce sun yi kame, bayan kutsen da magoya bayan na Wigan suka yi a fili

Shugaban Wigan David Sharpe ya ce kungiyar za ta yi aiki tare da hukumar kwalllon kafa ta Ingila da ‘yan sanda domin nazarin hotunan bidiyon yadda aka yi magoya bayansu suka kutsa tare da mamaye fili a lokacin da suka doke Manchester City 1-0 a ranar Litinin.

A yayin wannan kutse ne dan wasan City Sergio Aguero ya yi sa-in-sa da wani mai goyon baya, inda ya ce mutumin ne ya tofa masa yawu da kuma zaginsa.

Wasu magoya bayan na Wigan, a yayin murnar da ta sa su kutse cikin filin bayan da kungiyar tasu ta fitar da Manchester City a zagaye na biyar na gasar ta cin kofin FA, sun rika yage allunan talla da ke filin suna jefa wa ‘yan sanda.

Hukumar kula da wasan kwallon kafa ta Ingila FA, ta ce za ta yi nazarin rahoton alkalin wasan da ya jagoranci fafatawar da kuma hotunan bidiyon lamarin.

Wani babban jami’in ‘yan sandan Manchester Stuart Ellison ya ce kwallon kafa wasa ne na iyali, kuma duk wani abu na kokarin kawo cikas cikinsa ga ‘yan wasa ko kuma ‘yan kallo abu ne da ba za a yarda da shi ba.

A wata sanarwa da ya fitar babban jami’in kungiyar ta Wigan Jonathan Jackson ya ce kungiyar ta ji takaicin wannan abu da bai dace ba, wanda wasu ‘yan kalilan din magoya bayansu suka yi, kuma za su gudanar da cikakken bincike.

Sakamakon wasan dai ya kawo karshen fatan Manchester City na cin kofuna hudu a kakar nan, wadanda suka hada da na Premier da shi na FA, da na League, wanda aka yi wa lakabi da Carabao a bana da kuma na zakarun Turai.

Guingamp ta dauki dan Didier Drogba wasa


Isaac DrogbaHakkin mallakar hoto
GUINGAMP

Image caption

Burin Isaac Drogba shi ne ya zama dan wasan tawagar Ingila ta kasa

Dan tsohon dan wasan gaba na Chelsea Didier Drogba mai shekara 17 Isaac ya shiga kungiyar Guingamp ta gasar Ligue 1 ta Faransa.

Isaac Drogba, wanda kamar mahaifin nasa dan wasan gaba ne a da yana taka leda ne a kungiyar matasa ta Chelsea.

Matashin ya koma kungiyar ta Guingamp ne shekara 16 bayan babansa ya tafi kungiyar daga Lens a kan fam 80,000.

Didier Drogba, wanda ya ci kwallo 24 a wasa 50 da ya yi wa Guingamp, ya sanya wata sanarwa a shafinsa na Instagram cewa yana matukar alfahari da dan nasa Isaac Drogba.

Biyu daga cikin tsoffin abokanan wasansa a Chelsea, na daga wadanda suka aika masa da murnarsu da kuma fatan alheri kan wannan matsayi da dan nasa ya kai.

Tsoffin ‘yan wasan kuwa su ne Frank Lampard da kuma tsohon kyaftin din Chelsea John Terry.

Didier Drogba ya yi kasa da kaka biyu ne a Guingamp daga nan ya koma Marseille, inda a can kuma ya yi kasa da shekara daya kafin ya koma Chelsea a 2004.

A Chelsea din ne ya ci kofin Premier hudu, da na FA shi ma hudu da kuma na zakarun Turai, tare kuma da yi wa kasarsa Ivory Coast wasa sau 104.

A wata tattaunawa da aka yi da shi a shekara ta 2015 ya ce dan nasa wanda aka haifa a Faransa yana son ya zama dan wasan tawagar Ingila.

Nigeria: El-Rufai 'ya rushe gidan Sanata Hunkuyi'


Sai dai Gwamna El-Rufai ya ce an rushe gidan ne saboda ya saba ka'idodjin gine-gine.Hakkin mallakar hoto
TWITTER/HUNKUYI

Sanatan da ke wakiltar jihar Kaduna a majalisar dattawan Najeriya Suleiman Hunkuyi, ya yi zargin cewa gwamnan jihar Nasir El-Rufai ya rushe gidansa da ke jihar.

“Da sanyin safiyar yau [Talata] gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai da kansa ya tuka motar rusau tare da rakiyar tankokin yaki inda suka rushe gidana da ke lamba 11B a kan titin Sambo.

“Wannan shi ne iyakar wulakanci da kuma rashin rashin ya kamata, wanda ba a taba ganin irinsa ba a jihar Kaduna,” a cewar Sanata Hunkuyi, a wani sakon Twitter da ya wallafa.

Sai dai Gwamna El-Rufai ya ce an rushe gidan ne saboda ya saba ka’idojin gine-gine.

Wani sako da ya wallafa a shafin gwamnan Kaduna na Twitter ya ce: “An rushe wani gida a safiyar nan saboda ya keta dokokin gine-gine da kuma harajin kasa tun shekarar 2010.

“An mika filin da aka rushe hannun hukumar gine-gine domin mayar da shi wurin shakatawa.”

Hotuna da bidiyon da Sanata Hunkuyi ya wallafa ba su nuna Gwamna El-Rufai cikin motocin da ya yi ikirarin cewa yana ciki ba.

Gwamnan da dan majalisar ta dattawa sun sha fama da rikicin siyasa, lamarin da wasu ke gani shi ne musabbabin rusa gidan sanatan.

Gidan da aka rusa shi ne ofishin bangaren da ke hamayya da Gwamna El-Rufai na jam’iyyar APC.

Masu sharhi na gani rikicin da ke faruwa tsakanin gwamnan da wasu manyan ‘yan siyasar jihar, ciki har da Sanata Shehu Sani da Honourable Isa Ashiru, ka iya kawo wa jam’iyyar APC matsala a zaben 2019.

Hakkin mallakar hoto
TWITTER/HUNKUYI

An kama mutumin da ya ce kiran sallah na damunsa a Sadiyya


Tsokaci nasa ya janyo masa caccaka daga wurin masu amfani da shafukan intanet.Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Tsokaci nasa ya janyo masa caccaka daga wurin masu amfani da shafukan intanet.

Hukumomi a Saudiyya na binciken wani marubucin kasar bayan da ya ce masallatai sun yi yawa kuma kiran sallah na damunsa.

Binciken ka iya sa wa a hana mutumin, Mohammed al-Suhaimi, fitowa a kafafen watsa labarai ya yi magana.

Mohammed al-Suhaimi ya soki yadda ake gudanar da kiran sallah, yana mai cewa yawaita kisan sallar da kuma yadda masallatai daban-daban ke amfani da amsa-kuwwa (lasifika) wurin yin kiran yana hana mutane bacci da kuma damun kananan yara.

Marubucin, wanda ya yi suna wajen sassaucin ra’ayi, ya yi tsokacin ne lokacin da yake hira da wani gidan talbijin na kasashen Larabawa.

Tsokaci nasa ya janyo masa caccaka daga wurin masu amfani da shafukan intanet.

A baya dai, hukumomin Saudiyya sun sanya wasu matakai da suka umarci a rika rage karar lasifika lokacin kiran sallah.

Dakarun Syria sun yi wa 'yan tawaye luguden wuta


Luguden wutar da dakarun gwamnatin Syrian suka yi a Gabashin Ghouta da ke wajen birnin Damascus, wanda ke hannun ‘yan tawaye ya yi sanadin mutuwar mutane da dama, in ji masu fafutika.

Hakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Kananan yara na cikin wadanda aka jikkata

Kungiyar the Syrian Observatory for Human Rights ta ce an kashe akalla farar hula 98, ciki har da kananan yara 20, sakamakon luguden wutar da aka yi ta sama da roka ranar Litinin.

Kungiyar, wacce ke da mazauni a Birtaniya, ta kara da cewa an jikkata mutum akalla 470, wasunsu ma na halin rai-kwakwai-mutu-kwakwai.

Jami’an majalisar dinkin duniya sun ce lamarin da ke faruwa a kasar ya wuce abin da hankali zai dauka, suna masu yin kira a tsagaita wuta.

Mutum kusan 400,000 be ke zaune a Gabashin Ghouta, wanda aka yi wa kawanya tun shekarar 2013.

Anyi amannar cewa rundunar sojin Syria na shirin soma kai hare-hare ta kasa a yankin.

Yankin shi ne tunga ta karshe da ke hannun ‘yan tawaye a wajen birnin Damascus.

Dakarun Syria sun matsa kaimi a yunkurin da suke yi na kwace yanki, inda rahotanni ke cewa sun kashe daruruan mutane tare da jikkata da dama.

Dalibai sun tserewa harin BH a Yobe


A shekarar 2016 ne wani bincike ya gano cewa har yanzu babu cikakken tsaro a makarantu a wasu jihohi da ke arewa maso gabashin NajeriyaHakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

A shekarar 2016 ne wani bincike ya gano cewa har yanzu babu cikakken tsaro a makarantu a wasu jihohi da ke arewa maso gabashin Najeriya

Wasu ‘yan mata ‘yan makaranta da malamansu sun kubuce wani hari da mayakan Boko su ka kai makarantar su a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya.

Shaidu sun ce wani ayarin mayakan Boko Haram ne cikin motocin akori kura su ka isa makarantar kwanan da ke garin Dapchi a jihar Yobe ranar Litinin.

Rahotanni sun ce mayakan sun yi harbe-harbe kuma sun tayar da abun fashewa.

Malaman da daliban sun tsere ne bayan da hayaniyar ta basu alamar cewa wani abu na faruwa a cikin gari.

Masu tada kayar bayan sun sace kayayyaki daga makarantar bayan sun tarar daliban da malaman su tsere.

Rahotanni sun ce an akie da karin jami’an tsaro zuwa garin.

A shekarar 2016 ne dai wani sabon bincike ya gano cewa har yanzu babu cikakken tsaro a makarantu a wasu jihohi dake arewa maso gabashin Najeriya, fiye da shekaru biyu bayan sace ‘yan matan Chibok.

Binciken wanda cibiyar bunkasa rayuwar mata, Women Advocate Research and Documentation Centre, da kuma Gender Equality, Peace and Development Centre suka gudanar, ya nuna babu ingantaccen tsaro na koyon karatu a makarantun gwamnati musamman a jihar Borno.

Saura kiris sojojin Nigeria su cafke Shekau suka janye


Abubakar Shekau ya ce kungiyarsa ce ta kai hari Maiduguri da wasu garuruwa a jahar Borno cikin 'yan kwanakin nan

Image caption

Abubakar Shekau ya ce kungiyarsa ce ta kai hari Maiduguri da wasu garuruwa a jahar Borno cikin ‘yan kwanakin nan

BBC ta samu labarin cewa saura kiris sojojin Nigeria su cafke jagoran kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau a wani farmaki da aka dakatar da su.

A wani faifen bidiyo da BBC ta samu daga hannun wasu dake fafutika tare da sojojin Najeriyar, an ga yadda sojojin ke kaiwa da komowa a wasu sansanoni na wucin gadi a dajin Sambisa.

Sai dai bayan kwana hudu da dakatar da sojojin daga ci gaba da kai farmakin, mayakan Boko Haram cikin motoci dauke da abubuwa masu fashewa sun kai wa sojojin hari.

An kashe sojojin Nigeria dana Kamaru 7 wasu kuma da dama suka samu raunuka inda kuma aka lalala motocin sojojin da dama.

Sai dai mako guda bayan sojojin sun shiga sansanin da Shekau yake boye sun tarar ya riga ya tsere.

A halin yanzu rundunar sojin Nigeria ta ce za ta bada takuicin dala $8,000 ga duk wanda ya bata bayanai da zasu kaiga kamo jagoran kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau.

Rundunar sojin Nigeria dai ta sha nanata cewa ta cafke ko ta kashe ‘yan kungiyar, inda kuma a wani taron manema labaru a Maiduguri, rundunar ta zayyana makaman da ta ce ta kwace daga mayakan Boko Haram.

Hotunan yadda ake rayuwa bayan annobar Ebola


Shekara hudu kenan tun bayan da aka ba da rahoton barkewar cutar Ebola a kasashen Liberia, Guinea da Saliyo da ke Yammacin Afirka.

Mai daukar hotuna Hugh Kinsella Cunningham ya koma kasar domin duba rayuwar mutanen da wannan annoba ta shafa.

An aerial view of West Point, Monrovia, Liberia.Hakkin mallakar hoto
Hugh Kinsella Cunningham

Mutane da cutar ta kashe lokacin da ta barke a 2014 sun zarce mutanen da ta kashe tun lokacin da ta soma barkewar a 1976.

Cutar ta fi yin tasiri a yankunan talakawa irinsu yankin Liberia, inda, ga mutane da dama, samun abincin da mutum zai sa a bakin sallati ma ba karamin aiki ba ne.

West Point wani yanki ne mai cike da jama’a a birnin Monrovia. An gudanar da tarzoma lokacin da gwamnati ta rufe yankin sannan ta killace mutane da suka kamu da cutar.

Eva Nah pictured outside her house in West Point, Monrovia, Liberia.Hakkin mallakar hoto
Hugh Kinsella Cunningham

‘Yan sanda sun kashe jikan Eva Nah lokacin da yake zanga-zanga saboda killace mutane da gwamnati ta yi. “Babu abin da yake son yi kamar buga tamaula da kuma zaman makanike,” in ji ta. “Mahaifi da mahaifiyarsa sun mutu don haka ni kadai ce danginsa.”

Shekaru bayan mutuwar tasa, an bai wa Eva diyyar kisansa abin da ya ba ta damar tura sauran yara hudu na danginta makaranta.

‘Yar uwar Rita Carol na cikin wadanda Ebola ta kashe. Ta taba sayar da abinci a kan wata hanya da ke West Point sai dai ta tara kudin da ta sayi firinji sannan ta soma kasuwancin kankara, inda take fatan rayuarta za ta inganta.

Rita Carol in her home in West Point, Monrovia.Hakkin mallakar hoto
Hugh Kinsella Cunningham

Etta Roberts works as a nurse at the Kahweh clinic.Hakkin mallakar hoto
Hugh Kinsella Cunningham

Etta Roberts ma’aikaciyar jinya ce a asibitin Kahweh da ke gabashin Monrovia. Akasari tana duba marasa lafiya 10 wadanda ke fama da zazzabi da kuraje.

Mutumin da ya bude asibitin, Reginald Kahweh, ya bude cibiyar kula da masu cutar Ebola bayan ya mahaifansa sun mutu sakamakon cutar, yana mai cewa: “Dole kowa ya dauki matakin da zai inganta al’uma… an gina wannan waje ne domin tunawa da wadanda suka mutu.”

A doctor at the West Point medical clinic.Hakkin mallakar hoto
Hugh Kinsella Cunningham

Annobar ta Ebola ta ggirgiza tsarin kiwon lafiyar Liberia inda kayan aiki suka kare. Dama dai kasar ba ta da ingantaccen tsarin kiwon lafiya saboda yakin basarar da aka kwashe shekara 14 ana yi.

Don haka ne ake sanya ido sosai kan yankuna kamar West Point inda ma’aikatan cibiyar kula da lafiya ta kasar ke sa ido ba dare ba rana ko da wani abu zai faru.

Swamps in Bong County, Liberia.Hakkin mallakar hoto
Hugh Kinsella Cunningham

J Roberts in his washing facilityHakkin mallakar hoto
Hugh Kinsella Cunningham

J Roberts na zaune a yankin na West Point wanda ke fama da zaizayar kasa. Ya soma kasuwanci bayan matarsa ta mutu sakamakon Ebola. “An kona gawar matata, ba binne ta aka yi ba don haka ji nake kamar ba zan sake ganinta ba. Na yanke shawarar ba da kulawa ga ‘ya’yanmu hudu,” in ji shi.

Yana sayar da ruwan zafi. Wannan sana’a na da matukar muhimmanci saboda rashin tsaftar da ake fama da ita a cikin al’umarsu.

Cross on a hill in Waterloo district, Sierra Leone.Hakkin mallakar hoto
Hugh Kinsella Cunningham

Duk da tagomashin da tsarin kiwon lafiyar kasar ya samu da kuma fatan mutanen da lamarin ya shafa ke da shi na ci gaba da gudanar da rayuwa, da dama daga cikin ma’aikatan da suka rika binne gawarwaki na cikin tsaka mai wuya.

Akasarin ma’aikatan talakawa ne shi ya sa suka yi murnar da aka ba su aikin.

Waterloo Ebola Graveyard. Sierra Leone.Hakkin mallakar hoto
Hugh Kinsella Cunningham

Mohammed Kanu, a former frontline worker during the Ebola crisis at Waterloo Ebola Graveyard. Sierra Leone.Hakkin mallakar hoto
Hugh Kinsella Cunningham

Gwamnati ta dauki Mohammed Kanu a matsayin mutumin da zai rika binne gawarwakin ba tare da matsala ba. Bai sake samun wani aiki ba shi ya sa ya koma kulka da tsirrai.

Bukukuwan da aka rika yi lokutan binne gawarwakin sun taimaka wurin yada cutar kuma an rika tsangwamar mutane da dama suka yi aikin binne gawarwaki.

Morla Kargbo, wani tsohon ma’aikacin binne gawa, ya yi bayani: “Mutane ba sa son ba mu hayar gida saboda sun san mun yi aikin binne mutanen da suka kamu da Ebola.”

A graveyard worker with his back to the camera walks through Waterloo Ebola Graveyard. Sierra Leone.Hakkin mallakar hoto
Hugh Kinsella Cunningham

Dukkan hotunan nan na Hugh Kinsella Cunningham ne.

Wigan ta fitar da Man City a FA


WiganHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Karo na uku ke nan da Wigan ke fitr da City a FA a kaka shida

Wigan Athletic ta taka wa Manchester City burki inda ta yi waje da ita a gasar FA a zagaye na hudu da suka fafata a daren litinin.

Will Grigg ne ya ci wa Wigan kwallo a ragar Manchester City ana saura minti 11 a tashi wasan.

Wigan da ke buga gasar lig one mataki na uku a Ingila ta samu sa’ar fitar da City ne a FA bayan jan katin da aka ba dan wasan City Fabian Delph tun kafin hutun rabin lokaci.

Karo na uku ke nan da Wigan ke fitar City a gasar FA a kakar wasanni shida.

Kungiyoyin premier uku ke nan suka sha kashi a gidan Wigan bayan doke Manchester City.

Ba mu yi wa Conte tawaye ba – Hazard


ChelseaHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Antonio Conte na fuskantar barazana a Chelsea

Eden Hazard dan wasan Chelsea ya ce a iya saninsa ba ya jin akwai wani dan wasa a kulub din da ke adawa da Antonio Conte.

Wannan na zuwa a yayin da wasu ke ganin sakamakon wasannin da Chelsea za ta buga da Barcelona a gasar zakarun Turai da kuma haduwarta da Manchester United a ranar lahadi a gasar premier su za su tantance makomar Antonio Conte.

Amma Hazard ya ce suna bayan kocinsu, kuma abin da suka sa a gaba shi ne darewa saman tebur tare da doke Barcelona.

Chelsea dai ta sha kashi ci 4-1 a gidan Watford a gasar premier, kafin ta huce a kan West Brom, nasarar da ta ba ta haurowa matsayi na hudu tebur.

Chelsea ta kai zagayen kwata fainal bayan ta doke Hull City 4-0 a gasar FA da suka fafata a ranar Juma’a.

Yanzu kuma Chelsea na shirin karbar bakuncin Bacelona a stamford Bridge karawar farko a ranar talata kafin a san matsayin kungiyoyi biyu a karawa ta biyu a gidan Barcelona.

Ko Chelsea za ta ji tsoron Barcelona?


Messi na BarcelonaHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Lionel Messi ya gaza cin Chelsea a haduwarsa 8 da kungiyar.

Chelsea ta dade tana ba Barcelona ciwon kai a gasar zakarun Turai, kuma rabon da Barcelona ta ci Chelsea tun kakar 2005/06.

Tsawon Watanni 16 rabon da Barcelona ta kawo ziyara a Ingila tun lokacin da ta sha kashi ci 3-1 a gidan Manchester City a watan Nuwamban 2016.

Sai dai wannan tarihi ne a baya, yayin da ake ganin tsarin Barcelona ya canza karkashin abon kocinta Ernesto Valverde wanda ke farautar lashe kofuna uku a kakar bana.

Duk da cewa mai yiyuwa Barcelona ba za ta taka leda kamar a lokacin Pep Guardiola ba, amma yadda kungiyar ke wasa a yanzu ana ganin ta shirya haduwa da Chelsea a gasar cin kofin zakarun Turai domin Barcelona na da kyau a yanzu.

A bana Barcelona ta sake kafa tarihin da Guardiola ya kafa a 2010 inda ta buga wasanni 31 a Lig ba tare da an samu galabarta ba.

Ko da yake a tarihi Chelsea na cikin kungiyoyin Ingila da dodon Barcelona Lionel Messi ya gaza ci a haduwarsa 8 da kungiyar.

Messi ya taba barar da fanariti a wasan dab da na karshe da Chelsea ta fitar da Barcelona, inda a kakar ne Chelsea ta tafi ta lashe kofin a Munich, zamanin Roberto Di Matteo.

Sai dai a bana ana ganin labari na iya sauyawa domin kakar bana Messi ya ci kwallaye 27 a dukkanin wasannin da Barcelona ta buga.

Ana ganin babu wasu abokan hamayya da ke iya takawa Messi burki, watakila sai dai karfen raga inda a bana Messi ya daki karfe sau 15.

Ko da yake gwalkifan Chelsea Thibaut Courtois ya sha taka wa Messi burki tun lokacin da yana tsaron ragar Atletico Madrid.

Messi ya kasa cin Courtois a haduwa shida da suka yi a La liga a kakar 2013-14, kakar Courtois ta karshe a tsohuwar kungiyarsa Atletico Madrid.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Chelsea ta taba lashe kofin zakarun Turai bayan ta fitar da Barcelona a 2012

Manajan Chelsea Antonio Conte ya ce sai idan sun taka leda a tsanake idan har za su iya doke Barcelona.

Chelsea dai ta farfado ne daga matsalolin da ta fuskanta a makwannin baya, inda ta samu nasara a jere a wasannin gasar FA da ta doke West Brom da Hull City.

Bayan Chelsea ta hadu da Barcelona a gasar zakarun Turai a ranar Talata, za ta sake haduwa da Manchester United a ranar lahadi a gasar premier.

Tarihin Haduwar Barcelona da Chelsea a gasar zakarun Turai

 • Barcelona 2 Chelsea 2 – 2011/12 gzagayen dab a karshe haduwa ta biyu
 • Chelsea 1 Barcelona 0 – 2011/12 zagayen dab a karshe haduwa farko
 • Chelsea 1 Barcelona 1 – 2008/09 zagayen dab a karshe haduwa ta biyu
 • Barcelona 0 Chelsea 0 – 2008/09 zagayen dab a karshe haduwar farko
 • Barcelona 2 Chelsea 2 – 2006/07 rukunin farko
 • Chelsea 1 Barcelona 0 – 2006/07 rukunin farko
 • Barcelona 1 Chelsea 1 – 2005/06 zagayen kungiyoyi 16
 • Chelsea 1 Barcelona 2 – 2005/06 zagayen kungiyoyi 16
 • Chelsea 4 Barcelona 2 – 2004/05 zagayen kungiyoyi 16
 • Barcelona 2 Chelsea 1 – 2004/05 zagayen kungiyoyin 16
 • Barcelona 5 Chelsea 1 – 1999/2000 kwata fainal haduwa ta biyu
 • Chelsea 3 Barcelona 1 – 1999/2000 kwata fainal haduwa ta fako.

'Gyaran motar Boko Haram ya sa mun shekara 8 cikin ukuba'


Nigerian Islamist extremist group Boko Haram pictured with the leader of the Nigerian Islamist extremist group Boko Haram, Abubakar Shekau (C).Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Dubban wadanda ake zargi da Boko Haram suna tsare

A lokacin da wasu kanikawa masu gyaran mota Taye da Kehinde Hamza suka karbi gyaran wata mota a shagonsu da ke jihar Bauchi a Najeriya cikin shkarar 2010, ba su taba tsammanin za su shafe shekara bakwai cikin ukubu ba.

Ashe ba su san cewa motar ta wani mayakin boko Haram ba ce, kuma gyaranta da suka yi ya sa aka kama ‘yan biyun.

Sai da suka shafe shekara takwas kafin su samu ‘yancinsu, inda aka sake su tare da wasu mutum 473 da ake tuhuma da ayyukan ta’addanci.

Labarinsu daban yake daga cikin dumbin mutanen da ake ci gaba da yi musu shari’a.

Alkalai hudu ke sauraron kararrakin tun Litinin din makon da ya gabata a garin Ka’inji da ke jihar Naija a tsakiyar kasar.

Zuwa yanzu dai wadanda ake sake sakamakon rashin kwararan shaidu sun fi yawa a kan wadanda aka samu da hannu a kungiyar aka kuma yanke musu hukunci.

Ta auri dan Boko Haram tana da shekara 11

Mafi yawan wadanda aka sallama a makon da ya gabata sun hada da yara da tsofaffi.

Wasu kuwa kamar Taye da Kehinde sun kasance a tsare ne tun shekarar 2010.

Mariam Mohammed kuwa ‘yar kabilar Shua Arab daga jihar Borno State, sojoji ne suka kama ta a yayin da take neman tserewa zuwa dajin Sambisa – sansanin ‘yan Boko Haram a shekarar 2014.

Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Wannan yarinyar na daya daga cikin miliyoyin mutanen da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu

Ta kallafa ran son zuwa dajin ne aka kuma aurar da ita ga wani mayakin kungiyar a lokacin da take da shekara 11, a cewar wata sanarwa daga ma’aikatar shari’a ta Najeriya.

A makon da ya gabata ne, ta bayyana a kotu da jaririnta dan wata uku.

Har yanzu dai ba a san irin tasirin da dadewar da suka yi a tsare ta yi musu ba.

Ma’aikatar shari’ar ta ce wasun su suna fama da ciwon hauka, duk da cewa ba a tabbatar da ko suna tare da ciwon ba ne tun kafin a tsare su.

A shari’ar da aka yi a watan Oktobar 2017, an saki fiye da mutum 400 da ake zargi, inda aka yankewa 45 hukuncin dauri saboda rawar da suka taka a kungiyar Boko Haram, wadda ta yi sanadin mutuwar fiye da mutum 20,000 tare da raba miliyoyin mutane da muhallansu.

Wanda ya kitsa sace ‘yan matan Chibok

Ministan shari’a na Najeriya Abubakar Malami ya shaida wa BBC cewa za a kai wadanda aka sallama din cibiyar sauya tunani kafin daga bisani a mika su ga muhallansu.

Amma a yayin da wadannan alkalan suke kokarin ganin an yankewa wadanda ake tuhuma hukunci, akwai kuma wasu mutum 5,000 din sa suke jiran a saka musu ranar da za a yi tasu shari’ar.

Alkalan sun gano mutum 205 da ke da laifi wajen hannu a laifukan da suka shafi ta’addanci, da suka hada da ‘kitsa’ sace ‘yan matan sakandaren Chibok.

Tun da farko alkalai sun samu Haruna Yahaya, wani mai shekara 35 da hannu wajen kitsa sace ‘yan matan sakandaren Chibok a 2014, duk da ya musanta cewa bai aikata hakan bisa son rai ba.

A ranar Juma’a, suka kara masa tsawon zama a gidan yari saboda shirya sace ‘yan matan.

An yanke masa hukuncin zaman gidan yari na shekara 30.

Amma a yayin da ake sa ran irin wadannan hukunci za su zama sakayya ga mutanen da rikicin Boko Haram ya shafa, kungiyar da ke kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta saka ayar tambaya kan yadda ake gudanar da shari’ar.

Kungiyar ta sha gabatar da hujjoji da ke nuna yadda dakarun tsaro suka tsare daruruwan matasa a matsayin mayakan Boko Haram ba tare da wasu kwararan hujjoji ba.

Hukumomin Najeriya sun sha nanata cewa ana yi wa wadanda ake tuhuma adalci a wajen gabatar da shari’ar da kuma samar musu lauyoyin da ke kare su.

Japan na shirin yin ginin katako mafi tsawo a duniya a Tokyo


Wooden skyscraperHakkin mallakar hoto
Sumitomo Forestry

Wani kamfanin kasar Japan yana shirin yin ginin katako mafi tsawo a duniya, domin yin bikin cikarta shekara 350 da zamowa kasa a shekarar 2041.

Kamfanin Sumitomo Forestry ya ce kashi 10 cikin 100 na ginin mai hawa 70 zai kasance na karfe ne, da za a hada da katako kubik mita 180,000, wanda zai isa a gina gidaje 8,000, za a kuma shuka bishiyoyi da ciyayi a ko wanne hawa.

Kamfanin ya ce ginin zai kasance mai jurewa girgizar kasa da karfin iska, kuma hakan zai sa ya kare shi daga yawan girgizar kasar da ake yi a birnin tokyo.

Kuidn da aka kiyasta za a kashe wajen yin ginin ya kai daka biliyan 4.02.

Amma kamfanin Sumitomo ya ce yana sa ran kudin zai ragu kafin a kammala ginin saboda sauyen-sauen ci gaban fasaha da ake samu.

Jaridar Guardian ta ruwaito cewa a yanzu haka wani gini mai tsawon mita 53 da yake birnin Vancouver ne gini na katako mafi tsawo a duniya.

Za a yi amfani da ginin W350 wajen mayar da shi ofisoshi da shaguna da kuma gidaje.

Arsenal da Emirates sun sabunta yarjejeniya


ArsenalHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Kawancen Arsenal da Emirates da aka fara a 2006 yanzu zai kai har zuwa shekaru 18

Kamfanin jirgin sama na Emirates, ya sabunta yarjejeniya tsakaninsa da Arsenal kan daukar nauyin tufafin kulub din.

Arsenal da Emirates sun tsawaita yarjejeniya tsakaninsu ta shekaru biyar, a yau litinin.

An bayyana cewa girman yarjejeniyar ta kai fan miliyan 200.

Arsenal za ta ci gaba da amfani a sunan Emirates a tufafinta har zuwa karshen kakar 2023-24.

Yarjejeniyar daukar nauyin tufafin ita ce mafi girma da Arsenal ta taba amincewa, kuma kawancen Arsenal da Emirates da aka fara a 2006 yanzu zai kai har zuwa akalla shekaru 18.

Arsenal ta ce yarjejeniyar ci gabanta ne ta fuskar zuba jari kuma kamfanin Emirates zai taimakawa kulub din ga kishirwar lashe kofi.

Karkashin sabuwar yarjejeniyar, Arsenal za ta yi amfani da jirgin Emirates a lokacin wasannin share fagen kaka.

Sannan filin wasan Arsenal zai ci gaba da amfani da sunan Emirates har zuwa 2028, karkashin yarjejeniyar da bangarorin biyu suka amince a 2012.

Yarjejeniya tsakanin Arsenal da Emirates ita ce mafi girma a Ingila, amma har yanzu akwai tazara tsakaninsu da kawance tsakanin kulub din PSV Eindhoven na Holland da kuma kamfanin Philips.

Ana tilasta wa 'mayu' shan fitsarin mutum a India


Ana zargin matan biyu da maita

Image caption

Jami’ai a yankin sun bai wa matan wani kati bayan samun labarin abin da ya faru

‘Yan sanda a India sun kama mutum 11 da laifin cin zarafin mata biyu a kudancin jihar Jharkhand sakamakon zargin su da maita.

An yi wa matar mai shekara 65 da ‘yarta mai shekara 35 tsirara, tare da aske musu gashi sannan aka zagaya da su tituna har da kasuwannin kauyen, tare da tilasta musu cin kashin bil adama.

Matashiyar ta shaida wa BBC cewa ana zargin ta da mahaifiyarta da yada wata cuta a kauyen.

Zargin maita dai ba wani sabon abu ba ne a wasu yankunan kasar India, musamman ga mata.

Kwararru sun ce camfin da mutane ke yi kan maita na kara sanya rayuwar mutane cikin hadari, wasu matan da maza suka mutu kan fuskanci irin wannan matsalar musamman idan ana son cinye musu gadon filaye ko kuma gonaki.

Uwa da ‘yar sun tafka kuskuren tuntubar wani likita da bai kware ba a lokacin da wani dan uwansu ya mutu, shi kuma ya dora alhakin mutuwar akansu.

”Washegari ne aka hukunta mu,” in ji ‘yar matar.

Duk da sun ki amincewa da zargin da ake musu, sai da ‘yan uwansu suka taru aka tasa keyarsu zuwa wani fili aka kuma watsa musu fitsari a fuska, tare da tilasta musu hadiye fitsarin ta hanyar dura.

Mutane sun taru suna kallonsu da yin tofin alla-tsine a lokacin da aka zagaya da su kasuwa tsirara.

Matan biyu sun sha bakar wahala, babu kuma wanda ya zo don taimaka musu.

‘Yan sandan yankin sun ce sun fara wani shirin gangamin wayar da kan al’umma, musamman na yankunan karkara, don magance sake faruwar haka nan gaba, sannan sun bai wa matan kariya.

Nigeria: An yi jana'izar Sheikh Abubakar Tureta


TuretaHakkin mallakar hoto
Nurah Ringim

Image caption

Sheikh Tureta ya mutu yana da shekara 74 a duniya

Allah ya yi wa sanannen malamin nan na addinin musulunci da ke Kaduna a arewacin Najeriya Sheikh Abubakar Tureta rasuwa.

Malamin ya rasu ne a ranar Lahadi a Asibitin Garkuwa da ke Kaduna.

Tuni dai aka yi jana’izar marigayin a ranar Litinin da safe a gidan sa da ke Tudun Wada layin Kosai.

Ya mutu yana da shekara 74 a duniya.

Takaitaccen tarihinsa

An haifi Sheikh Abubakar Tureta ranar 5 ga watan Janairun 1944, kuma dan asalin jihar Sokoto ne da ke arewa maso yammacin kasar.

Ya mutu ya bar mata uku da ‘ya’ya 39 da kuma jikoki 85.

Malamin yana daga cikin jiga-jigan malamin kungiyar Izalatul Bidi’a Wa Ikamatus Sunnah.

Ya taba rike shugabancin majalisar malamai na tsohuwar jihar Sokoto.

Dan wasan Kano Pillars Chinedu Udoji ya mutu a hatsarin mota


Chinedu UdojiHakkin mallakar hoto
Chindeu Udoji/Facebook

Image caption

Chinedu Udoji ya mutu ya bar mace daya da yara biyu

Dan wasan tsakiya na kulob din Kano Pillars, Chinedu Udoji, ya mutu sakamakon hatsarin mota.

Mai magana da yawun kungiyar Idris Rilwanu Malikawa Garu, ya ce hatsarin ya faru ne a ranar lahadi da daddare a kan titin Bompai da ke birnin Kano.

Garu ya ce, “Motar Udoji ta bugu ne a jikin ginin shatale-talen Independent Way, a kan hanyarsa ta komawa gidansa da ke unguwar Badawa, bayan ya kai wa wani abokinsa dan wasan tawagar EWnyimba ziyara a otal.

Udoji dai shi kadai ne a cikin motar yayin da hatsarin ya faru.

Udoji na cikin tawagar Kano Pillars a wasan da suka buga da Enyimba inda aka tashi 1-1 a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano.

Kulob din Kano Pillars ya ce yana aiki kan duk wasu takardu da ake bukata don kai gawar zuwa kauyen mamacin don binne shi.

Udoji dai ya mutu ya bar mata daya da ‘ya’ya biyu.

Me zai faru idan dabbobi suna da hankali irin na mutane?


Hakkin mallakar hoto
FRANS LANTINGSPL

30 Agusta 2016

Aika wannan shafi Facebook Aika wannan shafi Twitter Aika wannan shafi Messenger Aika wannan shafi Email Aika.

Idan duk halittar da ke fadin duniyar nan na da hankali irin namu, zamu hada kai ne ko kuma zamu yaki juna?

A fim din ‘Planet of the Apes’, wani mutum ya samu kansa a wata duniya da birrai masu hankali da tunani ke bautar da mutane. Pierre Boulle, wanda ya rubuta littafin a 1963 wanda daga baya aka mai da shi fim ya ce labarin na sa na cikin rukunin ‘in-da-ace’.

To me zai faru idan aka fadada hasashen, ya zama ba birrai ne kadai zasu yi irin tunanin mutane ba, har ma dukkan wata nau’in halitta dake duniya? Idan aka wayi gari duk dabbar da ke duniya ta zama mai hankali da tunani me zai faru?

Wata halittar za ta mulki ragowar ne kamar yadda mutane su ka yi ko kuma za a samu sasantawa ne a gudanar da rayuwa cikin daidaito da mutunta juna? Wannan dai batu ne da ba zai taba yiwuwa ba amma tattauna shi zai sa mu fahimci gaskiya game da dabi’ar bil’adama da kuma matsayinmu a duniya, na halittar da ta mallake dukkan halittu.

Abin takaicin shi ne, da hakan za ta faru da lamarin ba zai yi kyau ba: “Rikici ne zai barke a bankasa,” in ji Innes Cuthill, masanin dabi’ar zamantakewar halitta a jami’ar Bristol. “Mu daina dauka cewa hankali ya na sa kirki.”

Hakkin mallakar hoto
iStock

Image caption

Da yake birrai suna kama da mutane, za su iya samun wata dama fiye da sauran dabbobi

“Ai kashe juna zamu yi,” in ji Robin Dunbar, mai nazarin sassauyawar dabi’ar halittu a jami’ar Oxford. “Ba a san mutane da neman zaman lafiya ba idan suka hadu da jinsin mutanen da basu san su ba.”

Josep Call, mai ilimin kwatanta dabi’ar halittu a jami’ar St. Andrews ya amince da cewa. “Idan ka duba tarihin dan Adam, ba na jin mun yi shahara kan kulla abota. Ba mamaki yanzu mun dan sassauta fiye da kakanninmu na baya, amma duba duniyar a yanzu ka gaya man in har mutane jinsin lumana ne.”

Idan aka yi la’akari da dogon tarihin da mu ke da shi na hallaka wasu jinsin halittun har ma da ‘yan uwanmu mutane, babu wani dalili da ke nuna cewa mu, ko kuma duk wata dabba da ta samu irin tunaninmu za mu iya wata dabi’a sabanin wacce mu ke a kai.

A takaice dai, yakin duniya na uku ne zai barke. “Mu na da mummunar alaka tsakaninmu da bakin jinsi musamman wadanda mu ke kallonsu a matsayin barazana,” in ji Cuthill.

Hakkin mallakar hoto
iStock

Image caption

Kifayen Shark za su iya yin mulki ne kawai a cikin ruwa

Idan ko haka ne, wa zai yi nasara? Jinsina da yawa dai ba su da alamar nasara. Misali, duk dabbobin da ke cin tsirrai zalla, na bukatar bata lokaci da yawa wurin cin abinci da zai ishe su.

Don haka za su samu takaitaccen lokacin da za su sadar da bayanai a tsakaninsu, su kera ababen more rayuwa, su bunkasa al’adunsu ko kuma su yi yaki. Don haka dabbobin da ke cin abinci samfurin protein su ne za su yi zarra.

A cikinsu, kifayen ‘shark’, ‘dolphin’, da ‘whale’ su ma ba inda za su kai tun da iyakarsu cikin ruwa. Sai dai za su iya fafatawa tsakaninsu don samun mulkin cikin ruwan.

Haka kuma duk dabbobin da ba sa iya rayuwa sai a wasu kebantattun wurare kamar kurmi, ko hamada ba za su iya mulkar duniya ba. Manyan mafarauta irin su zaki, damisa, da kyarkyeci da ma wadanda ba sa farautar irin su giwa da mugun dawa su ne za’a fafata da su, kamar yadda ta faru a fim din ‘Jurassic Park.’

A farkon wayewarsu, su ne zasu zama babbar barazana gare mu. Da za’a tsiraita mu a jefa mu cikin dokar daji, tabbas su za su yi nasara akan mu. Amma kasancewar muna da makaman zamani, kuma mutane sun fi wadannan dangin halittun yawan al’umma, barazanar ta su ba za ta yi nisa ba kafin mu shafe su daga bayan kasa (abinda, a yanzu ma muke cikin yi wa jinsin halittu da yawa).

Kamar yadda Alex Kacelnik, masanina dabi’ar zamantakewar halittu a jami’ar Oxford ya ce: “Daga karshe dai mu zamu yi nasara.”

Amma fa da zarar mun kawar da manyan dabbobi masu cin nama, zamu fuskanci wadansu abokan adawar: ‘yan uwanmu makusanta, wato birrai. Kamar yadda Cuthill ya bayyana, kayayyakin fasaharmu sun taimaka matuka wurin ci gabanmu, kuma birrai na da halitta irin ta mu, wacce za ta basu damar amfani da fasaharmu.

Za su iya amfani da kwamfutocinmu, su rike bindigoginmu sannan su amfana da halittar jikinsu wacce tafi ta dan Adam kuzari. Haka kuma za su iya kirkiro na su kayan fasahar cikin gaggawa ta hanyar amfani da kayan fasahar mutane.

Hakkin mallakar hoto
iStock

Image caption

Dan adam ba shi da karfi kamar sauran dabbobi

Sai dai ‘yan uwanmu birrai zasu iya wadannan abubuwa ne kurum idan har za su iya samun tarin ilimin da mu ke da shin a yadda ake amfani da kayayyakin fasahar, yadda ake yaki, yadda za su fahimce mu – abokan gabarsu – da kuma sauran ilimai da dama.

Amfani da iliminmu domin amfaninsu shi ne hanya guda tilo da zasu iya bi wurin murkushe mu. Sai dai ba za su samu wadataccen lokacin da za su mallaki iliminmu kafin su ma mu kawar da su daga doron kasa. “Da ace za su samu duk ilimin da muke da shi to da za a yi canjaras tsakanin mutane da birrai,” in ji Call. “In kuwa ba haka ba, koda yake za su zamo babban kalubale gare mu, duk da haka ba zasu iya mallake duniya ba.”

Amma fa idan lokaci ya tsawaita, babban ginshikin mallakar duniya shi ne iya rayuwa cikin kowanne yanayi da muhalli. Hakika, wannan kwarewar na daga cikin sirrin daukar bil’adama a ban kasa.

Duk da dai asalinmu daga yanki mai dumi da yawan ciyayi mu ke, mun gano hanyoyi da dama na rayuwa a sassan duniya dabam-daban, kama daga tsaunuka zuwa hamadar kankara.

Haka kuma yawan adadi zai yi rana, da kuma kwarewa wurin iya buya.

Watau dai, alamomi na nuna cewa halittun ‘bacteria’ da sauran kananan halittu irinsu su ne za su gaje mulkin duniya – fiye da yadda su ke yi a yanzu. A’a ‘bacteria’ ba su da kwakwalwa don haka ba zata taba yiwuwa su samu hankali da tunani irin na mutane ba.

Amma dai gazawar tasu, alheri ne a gare mu, idan aka yi la’akari da yawansu. “Ko a yanzu ‘bacteria’ na ko’ina, har da cikin jikinmu,” in ji Call. “Da za su yi hankali da kuwa za su iya ganin bayanmu.”

“Ba zan yi mamaki ba idan wata karamar halitta dangin ‘virus’ ta mallake duniya,” in ji Dunbar.

“Mutane za su shiga cikin bala’i idan fada ya hado su da kananan halittu masu hankali da tunani,” in ji Call. “Matsalar ita ce, ba zamu iya kawar da su ba, saboda mu na bukatarsu domin ci gaba da rayuwa.”

Hakkin mallakar hoto
iStock

Image caption

Wace dabbace za ta gaji kasa bayan dan adam?

Koda an hallaka mutane baki daya, rikicin dai ba karewa zai yi ba. Babu wani dalili da zai sa mu yi tsammanin dabbobin da ke da hankali da tunani irin na mutane za su yi halayya dabam da wacce mu ke yi ta wurin murkashe sauran halittu da mallake su.

Haka kuma za a samu rikice-rikice cikin jinsin halittu guda. “Ku tuna cewa dabbobi ba sa magance matsaloli domin amfanin jinsinsu baki daya,” in ji Kacelnik. “Su na rigima da junansu ne domin amfanin kabilarsu ko iyalansu.”

Watau dai kusan babu wanda zai amfana idan kowacce halitta ta sami hankali da tunani irin na mutane. Duk lokacin da aka karar da wani jinsin halitta, muhallan da suke ciki za su ci gaba da lalacewa, babu wanda zai tsira sai dai masu kwarin rai irin su ‘bacteria’, kyankasai da ko gafiyoyi.

Kamar dai yadda Cuthill ya ce: “Duk jinsin halittar da aka bari a baya, za su bata duniyar ne kamar yadda mu ke yi a yanzu.”

Ya ce: “Ba na jin akwai wani jinsin halittu da za su fi mu tausayi da jin kai. Daidaiton da ake samu a rayuwar yanzu na faruwa ne saboda wani yafi wani karfi a duniya.”

Idan kan so ka karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. What will happen if all animals were as smart as us.

Yadda za ka daina yaudarar kanka


Hakkin mallakar hoto
Getty Images

31 Agusta 2016

Bazawara Eleanor Bain ta yi zaton ta hadu da namijin da ya dace da ita a rayuwa. Ta koma wani sabon birni, ta na neman sabon aiki domin fara sabuwar rayuwa da ‘ya’yanta mata biyu, lokacin da ta tsammaci ta yi sabon masoyi.

Sai dai kuma duk da ra’ayinsu ya zo daya akan abubuwa da dama, akwai kuma dimbin matsaloli da su ka dabaibaye sabuwar soyayyar. Wani lokacin idan rikici ya barke tsakaninsu sai su kwashe sa’o’i su na sa-in-sa.

Yanzu da ta ke tuna baya, Bain ta ce ita ta yaudari kanta game da soyayyar. “Ba wai ba na son ganin laifinsa ba ne,” in ji Bain. “Ba na iya gani ne kwata-kwata.” Ba ta yarda akwai matsala ba ko lokacin da kawayenta ke ce mata ba su dace da juna ba. “Na yi iya bakin kokarin nuna musu cewa babu wanda ya cancanci na rayuwa da shi kamarsa.”

Don me mu ke haka? Yaudarar kai wacce hanya ce ta kare kanmu daga gaskiya mai daci. Ita ce dalilin da ya sa mu kan yi ikirarin mu na da gaskiya amma kuma mu ke karya doka; ita ke sa mu gaya wa kanmu muna son wani abu, misali yin ritaya cikin arzikin rufin asiri amma mu rinka abubuwan da za su rusa burin, ita ke sa mu ci gaba da aiki a kamfanin da ake nuna mana wariya wurin karin girma.

Yaudarar kai na iya saukaka mana takaicin rayuwa, amma ta na tattare da mummunar illa, a cewar Cam Caldwell, farfesan ilimin shugabancin kamfanoni da ma’aikatu a jami’ar Purdue da ke Indiana, Amurka, wanda ke gudanar da bincike kan yaudarar kai tsawon shekaru masu yawa.

Ya bayyana yaudarar kai a matsayin “rike akidoji biyu masu karo da juna ba tare da amincewa akwai sabani tsakaninsu ba.”

Daya daga cikin illolin yaudarar kai shi ne ware kai daga cikin al’umma saboda yadda ka damu da kare ra’ayinka ya zarta kokarinka na fahimtar gaskiya, a cewar wani masanin halayyar dan Adam M Scott Peck, a wata makala da Caldwell ya rubuta.

Ga wadanda ke son su guji bonono; rufe kofa da barawo sai su tambayi kansu: Me ya fi illa – sanin matsalar da ke maka barazana a rayuwa ko kuma sakankacewa komai ya na tafiya daidai har sai matsalar ta jawo maka gagarumar asara a soyayya, ko kasuwanci ko wurin aiki?

Ko da yake amincewa kanka cewa ka na cikin matsala abu ne mai wuya musamman a lamuran da su ka shafi soyayya, yin biris da matsalar na iya jawo maka cutuwa a kusan kowanne fanni na rayuwarka.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Matakai uku ne

Mafi yawanmu kan yaudari kanmu a wasu lokuta a rayuwarmu. Dubi misali harkar kudi, inda ake tafiyar da komai keke-da-keke amma duk da haka akan samu mutanen da ke riya cewa kamar ba haka lamarin ya ke ba, a cewar Kathleen Gurney, shugabar kamfanin Financial Psychology Corporation, da ke Sarasota a jihar Florida, Amurka.

Ta ce har akantoci kan yaudari kansu game da kudi duk da tarin ilimin da su ke da shi na kididdigarsa. Alal misali, akwai wani akanta da ya yi asarar gidansa saboda gaza biyan bashin bankin akan kari.

“Yaudarar kai ta na da matakai uku,” in ji Gurney. Na farko shi ne rashin amincewa akwai matsala, kamar mutumin da baya biyan bashi akan kari.

Mataki na biyu shi ne; kankantawa. Ma’ana, mutum zai yarda cewa akwai matsala amma sai ya fara kame-kamen yadda zai nuna cewa ba ta da wani tasiri. “Da gaske ne hakan na faruwa, amma matukar dai ina biyan bashin daga baya, ai ba komai don ina makara.”

Matakin yaudarar kai na uku shi ne gociya. A wannan lokacin mutum zai amince akwai matsala, kuma ta na da illa amma sai ya goce wa daukar alhakinta. “Na sani, amma ai ba laifina ba ne, ayyuka ne su ka yi min yawa shi ya sa ban samu in biya basussuka kan kari.”

To ina mafita? A cewar Gurney neman shawarar abokai ko kwararrun masana ita ce babbar maganin yaudarar kai.

Bugu da kari, ka na iya rubuta abinda ka ke buri a rayuwa sannan ka rubuta me ka ke yi don cimma burin, sai ka kwatanta ka ga in da gaske ka dauki hanya.

Kwarin giwa Yaudarar kai ba a harkar kudi ko soyayya ta tsaya ba kawai. Ta kan addabi mutane da yawa a bakin aikinsu. Anan ma, ana iya ganin yadda buri da karatun wasikar jaki kan maye gurbin nazarin gaskiya da gaskiya.

Wannan shi ne abinda ya faru ga wata ma’aikaciyar banki da ta nemi shawarar Nadine Gimbel, mashawarciya kan harkokin aiki a Frankfurt, Jamus.

Ma’aikaciyar ta yi kukan cewa an ki yi mata karin girma duk da kwazon da ta ke yi a bakin aiki. Matar mai shekaru sama da 40 na jira ne shugabanninta su lura da kokarinta har su yaba mata da karin girma.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

“Yaudarar kanta ta ke yi da take zaton cewa wani dabam ne zai gano kokarinta,” in ji Gimbel, wacce ta shawarci matar ta rubuta abinda take bukata sannan ta sanar da shugaban sashin da ta ke aiki. “Hakan ta yi kuma shugaban ya amince da kara mata girma.”

Shawarar Gimbel ga masu fuskantar wariya ko rashin gamsuwa a wurin aiki ita ce, su tantance me su ke bukata su tunkari shugabanninsu ko kuma su bar aikin da bai biya musu bukatunsu.

“Sauyi wani bangare ne na rayuwa, amma mu kan guje shi saboda tsoro,” in je Gimbel. “A gaskiya dai mu kan yi nadamar abinda bamu aikata ba fiye da abinda mu ka yi. Bamu san inda zamu kai ba, in da bamu ji tsoro ba.”

Tabbas! Sanin gaskiya game da kanka dabam, aiki da ita kuma sai da juriya da karfin hali. Ga Bain, ba ta iya samun kwarin gwiwar kawo karshen dangantakarta da sabon masoyinta ba sai da ta ga cin mutuncin nasa har ya kai ga ‘ya’yanta.

“Amma fa da ciwo matuka,” in ji Bain wacce ta ce ji ta yi kamar ta gudu daga garin lokacin da ta gano irin zurfin yaudarar da ta yi wa kanta.

Idan kana so ka karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. How to stop lying to yourself.

Gwamnatin Nigeria ta tuhumi Shugaban EFCC Ibrahim Magu


Ibrahim MaguHakkin mallakar hoto
EFCC

Gwamnatin Najeriya ta tuhumi shugaban riko na hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar ta’annati, EFFC, Ibrahim Magu da babban lauyan kasar Mr. Festus Keyamo.

An tuhumi mutanen biyu ne saboda tuhuma kan cin hanci da suke yi wa shugaban kotun kula da da’ar ma’aikata, Mr. Danladi Yakubu Umar.

Kafar watsa labarai ta The PRNigeria ta ce ta samu wasika biyu na tuhuma da aka aike wa Magu and Keyamo.

A cikin wasikun, wadanda aka aike musu ranar 16 ga watan Fabrairu na shekarar 2018, an bukaci Ibrahim Magu ya aika da amsarsa ga ministan shari’a kafin ranar Talata, 20 ga watan Fabrairu.

Wasikar ta nemi shugaban na EFCC ya yi bayani kan dalilan da suka sanya shi ya tuhumi shugaban kotun kula da da’ar ma’aikata da laifin cin hanci da rashawa duk da yake sau biyu EFCC na wanke shi daga zarge-zargen cin hanci.

Kazalika, wasikar da aka aike wa Mr. Festus Keyamo SAN, wanda ake zargi da zama lauyan Ibrahim Magu, ta nemi ya yi mata bayani kan wanda ya sa shi ya shigar da kara kan Danladi Umar.

Ana zargin shugaban kotun kula da da’ar ma’aikatan ne da laifin cin hanci na N10m, ko da yake sau biyu ana wanke shi a shekarar 2015 da kuma 2016, a cewar The PRNigeria.

Taron adu'oin jagoran 'yan adawa a Zimbabwe


Taron adu'oin da aka yi a wani coci da ke Harare, ya samu halartar daruruwan mutane daga sassan kasar.Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Taron adu’oin da aka yi a wani coci da ke Harare, ya samu halartar daruruwan mutane daga sassan kasar.

Shugaban kasar Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa, ya bayyana ta’aziyyarsa bisa ga rashin da aka yi na jagoran ‘yan adawa, Morgan Changirai, wanda ya mutu sakamakon cutar kansa a makon da ya gabata.

Mr Mnangagwa, ya bayyana marigayin a matsayin wani muhimmi a siyasar kasar wanda kuma ya dace a rinka tunawa dashi a tarihin kasar.

Daga nan ya yi kira ga al’ummar kasar da su hadu domin nuna alhininsu ga babban rashin da aka yi.

Taron aduu’oin da aka yi a wani coci da ke Harare, ya samu halartar daruruwan mutane daga sassan kasar.

Kazalika daruruwan magoya bayan ‘yan adawar kasar sun taru a wajen cocin, sanye da jajayen kaya, launin jam’iyyar su.

A ranar 15 na watan da mu ke ciki Allah ya yi wa Tsvangirai rasuwa yana da shekara 65 a duniya.

A ranar Talata ne za a binne gawarsa a kauyensa da ke Buhera.

Iceland: Za a hukunta wanda ya yi wa dansa kaciya


Za a sanya dokar hana kaciyar maza a IcelandHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Za a sanya dokar hana kaciyar maza a Iceland

Wani shugaban addinin musulunci a Iceland, ya yi alawadai da shirin da ake yi a kasar na hana kaciyar maza a matsayin wani yancin da mutane suke da shi na yin addininsu.

Ahmad Saddeeq, wanda limami ne a wata cibiyar raya addini da kuma al’adu a kasar, ya shaidawa BBC cewa, yin kaciya na daga cikin koyin addinin musulunci, dan haka batun hana wa sam bai dace ba.

Wani kudurin doka da ke gaba majalisar dokokin kasar a yanzu, ya tanadi hukuncin daurin shekara shida ga duk iyayen da aka samu da yi wa ‘ya’yansu kaciya.

Wata likita na son a halatta kaciyar Mata

Tsoron kaciya ya hana ‘yan mata komawa gida a Kenya

Kasar Iceland, ta zamo kasa ta farko a tarayyar turai da za ta fara bullo da doka a kan daina kaciyar maza.

A cikin kudurin dokar, an bayyana cewa yawanci ana yi wa yaran kaciya ne a gida kuma ba mamaki ana amfani da kayan aikin da ba a tsaftace su ba.

Musulman da suke kasar dai tsiraru ne.

An soma watsa labaran BBC a harsunan Igbo da Yarbanci a Nigeria


Members of the BBC Igbo and Yoruba teams in Lagos, Nigera

Image caption

Za a rika watsa shirye-shiryensu a shafin intanet

Sashen watsa labarai zuwa kasashen duniya na BBC ya kaddamar da sassa biyu gamasu jin harsunan Igbo da Yoruba a Nigeria da Afirka ta Yamma.

Za a rika watsa shirye-shiryensu a shafin intanet da shafukan sada zumunta, akasari ga masu amfani da wayoyin salula.

Ana amfani harshen Igbo a kudu maso gabashin Najeriya, yayin da ake amfani da Yarbanci a kudu maso yammacin kasar da kuma kasashen Benin da Togo.

Sabbin sassan na cikin wadanda Sashen watsa labarai zuwa kasashen duniya na BBC ya kaddamar a shirinsa mafi girma tun shekarun 1940, sakamakon kudin da gwamnatin Birtaniya ta bai wa sashen a shekarar 2016.

Ana kadamar da sabbin sassa 12 na BBC a Africa da Asia jimulla.

Sashen watsa labarai zuwa kasashen duniya na BBC ya soma fadada shirye-shiryensa a Nigeria – kasar da ta fi kowacce yawan mutane a Africa wacce ke da harsuna sama da 200 – ne a bara inda aka kaddamar da Sashen BBC Pidgin, domin mutanen da ke magana da turancin buroka.

Pidgin harshe ne da ake magana da shi, wanda ba shi da wani tsari na rubutu.

Su kansu ma’aikatan da za su yi aiki a harsunan Igbo da Yarbanci na BBC sun fuskanci kalubale na tsarin rubutu da harsunan ga masu karanta labarai – har sai da ta kai ga neman shawarwarin malaman jami’a.

“Yarbanci ka iya rikita matasa masu karatu saboda yana da kalmomi irin daya masu ma’ana daban-daban, don haka sai ai mu yi amfani da jimloli masu sauki wurin isar da sako a gare su,” in ji editan Sashen Yarbanci, Temidayo Olofinsawo.

Kafofin watsa labarai na harsunan Igbo da Yarbanci ba su da yawa a Najeriya, don haka ne ake sa ran sassan biyu na BBC za su samu karbuwa a gida da wajen kasar.

Wannanne karon farko da za a rika wallafawa da kuma watsa labarai da harshen Igbo ga kasashen duniya,” a cewar Adline Okere, edita a Sashen Igbo na BBC.

“Igbos are known for their entrepreneurial spirit – and they are spread all over the world,” she says.

Wadanne labarai za su ba ku?

Sassan biyu za su rika bayar da labarai sau biyu a tsarin BBC Minute – labarai da rahotanni cikin murya a shafin intanet da shafukan zumunta.

Image caption

Ma’aikatan Sashen Yarbanci na BBC

Shugabar Afirka ta Yamma ta BBC, Oluwatoyosi Ogunseye, ta ce za a mayar da hankali ne kan labarai sahihai wadanda suka shafi al’umma.

“Bayar da labarai da kuma tattaunawa da masu sauraro a harsuna Igbo da Yarbanci abu ne mai nishadantarwa,” in ji ta.

“Muna da BBC Hausa [wadda aka fi sauraro a arewacin Najeriya] a shekaru aru-aru kuma mun ga tasirin hakan ga masu saurare.

“Najeriya na da al’adu da dama kuma haka ne ya sa BBC ta bai wa kowanne bangare damar jin ta bakinsa a kowacce kafa.”

An capke mutum 3 dangane da tashin hankalin da ya faru a Jihar Zamfara


Hukumar 'yan sanda ta ce mutane na bada hadin kai a binciken da ta ke yiHakkin mallakar hoto
facebook

Image caption

Hukumar ‘yan sanda ta ce mutane na bada hadin kai a binciken da ta ke yi

Hukumar ‘yan sanda a Nijeria ta ce ta kama wasu mutane uku da ake zargin suna da hannu a kashe kashen baya baya nan da aka yi a jihar Zamfara.

A cikin wata sanarwa da ke dauke da sa hannun kakakin hukumar ‘yan sanda CSP Jimoh Moshood ta ce mutanen na bada hadin kai a bincike da ‘yan sanda suke yi.

Ta ce da zarar ta kamala binciken da ta ke yi , za ta gurfanar da mutanen a gaban kotu.

Wadanda ake zargi sun hada Halilu Garba mai shekara 45 da Zubairu Marafa mai shekara 45 da kuma Nafi’u Badamasi mai shekara 40.

Kamen dai na zuwa ne ya yin da ‘yan Nigeria ke cigaba da tofa albarkacin bakinsu game da matsalar rashin tsaro a jihar ta Zamfara.

A baya baya nan ne babban supeton yan sanda Ibrahim Idris ya bada umurnin tura da karin da jamian ‘yan sanda 130 zuwa jihar ta Zamfara.

Sai dai wasu masana kan harkar tsaro sun nuna shaku kan tasirin da wannan mataki zai wajan dakile ayuikan masu wannan aika aikar.

Me yasa ake shan kwayar Tramadol?


Hakkin mallakar hoto
PIUS UTOMI EKPEI

Image caption

Shan kwayar Tramadol fiye da kima na haifar da matsala

Hukumomin yaki da shan miyagun kwayoyi da kuma hukumar Kwastam a Najeriya, sun fara aikin dakile shigo da kwayar Tramadol ta barauniyar hanya.

Bincike ya nuna cewa, shan kwayar fiye da kima na sa maye ga bil-adama, inda sakamakon hakan kuma za a iya aikata wasu abubuwa ba tare da sanin an aikata ba.

Likitoci kan bayar da kwayar Tramadol ne domin rage radadin ciwo, amma a yanzu ta na neman zama annoba a tsakanin matasa ko al’ummar da kan sha, ta yadda za suyi aiki fiye da karfinsu, wani sa’ilin ma har ta zamo cuta.

Kazalika likitoci sun ce, shan irin wadannan kwayoyi fiye da kima na iya lalata wasu sassa na jikin dan adam.

Likitoci dai kan umarci a sha kwayar Tramadol ne bisa ka’ida, to amma wasu na wuce gona da iri.

Wani matashi da ke shan kwayar ta Tramadol, ya shaida wa BBC cewa, yana sha ne domin yana jin kasala a wasu lokuta, don haka ya ke sha domin ya ji garau.

Nigeria: NAFDAC ta kama manyan motoci biyu cike da Tramadol

An ki daukar matasa aikin asibiti saboda shan kwaya a Kano

Ana dai yawan amfani da kwayar ne saboda farashinta bai taka kara ya karya ba.

Akasarin direbobin motocin haya da masu dakon kayayyaki na shan wannan kwaya saboda su ji garau.

Bincike ya nuna cewa yadda masu fasa kaurin kwayar suka fahimce karbuwar ta a wajen jama’a, za a iya cewa masu shigo da ita ta barauniyar hanya kasuwarsu ce ta bude.

Kofin FA: Kamfani ya bayar da hakuri kan kwallon Juan Mata


Hoton yadda JUan Mata ya ci kwallonHakkin mallakar hoto
Others

Image caption

Kamfanin ya bayar da hakuri da cewa an yi kuskure ba a yi amfani da hoton da ya dace ba wajen haramta kwallon

Kamfanin na’urar bidiyon da ake amfani da ita mai taimaka wa alkalin wasa wajen warware takaddama (VAR) a wasa ya bayar da hakuri kan abin da ya ce kuskren amfani da hoton da ba shi ne ba, wajen haramta kwallon da Juan Mata ya ci a wasan Man United da Huddersfield na kofin FA.

Kamfanin Hawkeye ya ce an samu kuskure ne wanda ya sa aka sanya wa alkalin wasa hoton da ba shi ne, wanda kuma ya yi amfani da shi wajen yanke hukuncin hana kwallon da cewa dan wasan ya yi satar gida.

A ranar Asabar ne bayan da Mata ya ci wa United bal ta biyu kafin a tafi hutun rabin lokaci, sai alkalin wasa Kevin Friend ya kasa kunne inda ya ji bayanin da na’urar ta turo masa, kuma bayan jira na kusan minti daya sai ya hana kwallon da cewa Mata ya yi satar gida.

A Ingila ana gwajin amfani da na’urar ne mai taimaka wa alkalin wasa warware takaddama a gasar cin kofin FA da na Carabao a wannan kakar.

An yaba amfani da na’urar bayan da ta haramta bal din da Kelechi Iheanacho ya ci wa Leicester, lokacin da suka doke Fleetwood 2-0, a wasan zagaye na uku na cin kofin FA a watan Janairu.

Amma kuma tsohon kociyan Ingila Alan Shearer ya soki amfani da na’urar bayan da ta kasa ba wa Chelsea fanareti lokacin wasan da suka sake na kofin FA da Norwich.

Jadawalin Kofin FA: Man Utd za ta kara da Brighton


Kociyan Brighton Chris Hughton da na Manchester United Jose MourinhoHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Brighton ta doke Coventry ta gasar League One 3-1 ranar Asabar, yayin da United ta ci Huddersfield 2-0

Manchester United za ta kara da Brighton a wasan dab da na kusa da karshe na cin kofin FA, kamar yadda kungiyoyin biyu suka yi wasan karshe na cin kofin a shekara ta 1983.

A wancan lokacin Manchester United ta dauki kofin bayan ta doke Brighton 4-0 a wasan da suka sake yi na biyu, kasancewar na farko sun tashi canjaras 2-2.

A jadawalin wasan Southampton za ta je gidan wadda za ta yi nasara a karawar da za a yi ranar Litinin din nan tsakanin Manchester City da Wigan, yayin da Leicester City da Chelsea za su fafata.

Wigan, ta biyu a teburin gasar League One, za ta hadu da Manchester City a ranar Litinin din nan (19:55 GMT).

Yayin da Leicester, da ta ci Sheffield United 1-0 ranar Juma’a, za ta karbi bakuncin Chelsea, wadda ita ma a ranar juma’ar a gidanta ta casa Hull City 4-0.

Idan aka samu gwani bayan karawa ta biyu tsakanin Tottenham da Rochdale, kungiyar da ta yi galaba za ta hadu da Sheffield Wednesday ko Swansea, wadanda su ma za su sake fafatawa kasancewar an kasa samun gwani a wasansu na ranar Asabar da suka yi canjaras ba ci (0-0).

Dukkanin wasannin na matakin dab da na kusa da karshe na cin kofin na FA za a yi su ne a watan Maris mai zuwa daga ranakun 16 zuwa 19.

Serie A: Juventus ta yi rikon kwarya bayan doke Torino 1-0


Alex Sandro lokacin da ya ci TorinoHakkin mallakar hoto
Others

Image caption

Cin da Alex Sandro ya yi ne ya sa Juventus ta koma ta daya a teburin Serie A, na dan lokaci

Juventus ta ga ta leko ta koma a jagorancin teburin gasar Serie A, a lokacin da ta doke Torino 1-0, a wasan hamayya na birnin Turin, ranar Lahadi.

Bal din da Alex Sandro ya ci a kashin wasan na farko, ita ta ba wa Juventus damar zama a saman teburin na dan lokaci, kafin Napoli ta doke SPAL 1-0, a karawarsu a ranar Lahadin.

Nasarar ta Juventus kyakkyawan martani ne na kungiyar ta kociya Massimiliano Allegri bayan mamakin da ta sha a hannun Tottenham, wadda ta yunkuro daga baya suka yi canjaras 2-2, a wasansu na cin kofin zakarun Turai, ranar Talata da ta wuce.

Wannan canjaras da suka yi, ta kawo karshen nasarar da suke yi ta goma a jere.

Raunin da dan wasan da ya fi ci wa Juventus din kwallo Gonzalo Higuain, ya ji a farkon wasan na Lahadi, bai kawo musu cikas ba, inda suka ci gaba da kai wa abokan hamayyar tasu hari ba kakkautawa.

Juventus ta biyu a tebur, wadda ke harin kofinta na Serie A na bakwai a jere, tana da maki biyu fiye da yadda take a daidai wannan lokacin a bara, yayin da ita kuwa Torino take ta tara a tebur a yanzu.

Kofin FA: Wankin hula ya kai Tottenham dare ta yi 2-2 da Rochdale


Steve Davies lokacin da yake rama ta biyuHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Steve Davies ya rama wa Rochdale kungiya ta karshen tebur a gasar League One bal ta biyu a wasan da ta rike wa daya daga cikin na gaba-gaba a Premier Tottenham wuya

Steve Davies ya jika wa Tottenham aiki da bal din da ya rama wa kungiyarsa ta gasar League One, Rochdale a wasan cin kofin FA, zagaye na biyar,suka tashi 2-2, sakamakon da ya sa dole sai sun sake karawa.

Henderson ne ya ci wa Rochdale bal din farko ana shirin tafiya hutun rabin lokaci a minti na 45, sannan bayan an dawo daga hutun ne a minti na 59 Lucas Moura ya rama wa Tottenham.

Sai kuma a minti na 88 Harry Kane ya kara wa Tottenham ta biyu, da bugun fanareti bayan da aka yi wa Dele Alli keta, wadda ita ce bal ta 34, da ya ci wa kungiyar a kakar nan.

Ana dab da tashi ne a cikin mintunan da aka kara bayan 90, na ramakon lokacin da aka bata sai Davies ya yi wa Tottenham barna ya rama wa Rochdale bal ta biyu, aka ta shi 2-2, sakamakon da ya sa dole kungiyoyin su sake haduwa wasa na biyu, a gidan Spurs din.

Diego Costa ya zama dodon-raga a Atletico Madrid da ta ci Bilbao 2-0


Diego Costa da 'yan kungiyarsa ta Atletico MadridHakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Karo na biyu ke nan da Diego Costa ya ke Atletico Madrid

Diego Costa ya ci bal dinsa ta biyar tun lokacin da ya sake komawa Atletico Madrid a wasan da suka doke Athletic Bilbao 2-0, ya kasance maki bakwai ne tazara tsakaninsu da jagorar La Liga, Barcelona.

A wasan da suka yi ranar Lahadin nan Kevin Gameiro ne ya fara daga raga a minti na 67, bayan da Antoine Griezmann ya sako masa bal din.

Daga nan ne kuma sai Costa wanda wasansa na takwas ke nan a kungiyar tun lokacin da ya koma daga Chelsea, ya ci ta biyu cikin ruwan sanyi a minti na 80, da bal din da Kevin Gameiro ya zura masa.

Kafin wasan na Atletico Madrid da Athletic Bilbao a ranar Lahadin abokan hamayyar Bilbao Real Sociedad sun yi nasarar doke Levante 3-0.

Da karfe tara saura kwata na dare ne agogon Najeriya da Nijar na Lahadin ta hudu a tebur Real Madrid, wadda maki 13 ne tsakaninta da Atletico za ta fafata a gidan Real Betis.

Damben Shamsu Kanin Emi da Shagon Aleka


Dambe 10 aka yi a gidan wasa na Ali Zuma dake unguwar Dei-Dei a Abuja, Nigeria a safiyar Lahadi.

Mohammed Abdu ne ya hada wannan rahoton

Cikin wasannin har da wanda Shamsu Kanin Emi daga Arewa ya buge Shagon Aleka daga Kudu a turmin farko.

Damben da ya yi kisa shi ne wanda Shagon Jimama daga Kudu ya doke Garkuwan Sojan Kyallu Guramada a turmin farko, da wanda Shagon Dogon Auta daga Kudu ya buge Shagon Garba Dan Malumfashi daga Arewa.

Da wasan da Bahagon Ummarun Gundumi ya buge Nokiyar Dogon Sani daga Arewa.

Sai wasannin da aka tashi canjaras:

 • Shagaon Hussaini Na Barkoji da Shagon Ummarun Gundumi Guramada
 • Shagon Shagon Lawwalin Gusau daga Arewa da Bahagon Sama’ila daga Kudu
 • Shagon Bahagon Dan Kanawa daga Kudu da Shagon Shamsu daga Arewa
 • Shagon Alhazai daga Arewa da Danladi Na Dutsen Mari Guramada
 • Shagon Bahagon Fandam daga Kudu da Shagon Bahagon Musan Kaduna daga Arewa
 • Shagon Bahagon Fandam daga Kudu da Dogon Washa Guramada

Kotun Nigeria ta saki 'yan 'Boko Haram' 475


Kotuna hudu ne ke yi wa mutane 1,669 shari'a kan zarge-zargen hannu a rikicin Boko Haram.Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Kotuna hudu ne ke yi wa mutane 1,669 shari’a kan zarge-zargen hannu a rikicin Boko Haram.

Wata kotun Najeriya ta saki mutum 475 da ake zargi da kasancewa mambobin Boko Haram bayan da aka gano ba su da alaka da kungiyar.

Wata sanarwa da ofishin ministan shari’ar kasar, Abubakar Malami, ya fitar ta ce kotun da ke yin shari’a ga mutanen da ake zargi da shiga Boko Haram wacce ke zamanta a sansanin sojin Kainji na jihar Naija ce ta sallami mutanen ranar Juma’a.

Kakakin ministan, Salihu Othman Isah, ya ce za a kai mutanen wurin gwamnatocin jihohinsu domin a ba su shawarwari da kuma inganta rayuwarsu kafin a mika su ga ‘yan uwansu.

A cewarsa, “Cikin mutanen da aka kama har da wata yarinya wacce ke da jaririya ‘yar wata uku daga jihar Borno, wacce dan uwanta ya mika ta ga ‘yan Boko Haram suka aurar da ita ga abokinsa lokacin tana da shekara 11. An kama ta a 2014 lokacin da take yunkurin tserewa.”

Sanarwar ta kara da cewa an kama akasarin mutanen ne saboda zarginsu da kasancewa ‘yan Boko Haram ko kuma kin bayar da bayani kan yadda za a kama ‘yan kungiyar.

“Sai dai masu shigar da kara ba su iya tuhumarsu da kowanne laifi ba saboda ba a samu gamsassun shaidu da suka nuna su ‘yan Boko Haram ne ba. Don haka ne aka sake su,” in ji Salihu Othman Isah

Kafin sakin mutum 475 ranar Juma’a, sai da aka saki mutum 468 da ake zargi da zama mambobin Boko Haram bayan an gano ba su da alaka da kungiyar; sannan an yanke hukuncin daurin daga shekara biyu zuwa 15 ga ‘yan kungiyar 45.

A makon jiya kotun ta Najeriya ta yanke hukuncin daurin shekara 60 kan wani dan kungiyar ta Boko Haram.

Mutumin, mai suna Abba Umar, mai shekara 22, wanda kuma kwamanda kungiyar ne ya ce bai yi nadamar zaman dan kungiyar Boko Haram ba.

Wannan ita ce shari’a mafi girma da ake yi wa mutanen da ake zargi da kasancewa mambobin Boko Haram tun lokacin da kungiyar ta soma tayar da kayar baya.

Kotuna hudu ne ke yi wa mutum 1,669 shari’a kan zarge-zargen hannu a rikicin Boko Haram.

Hikayata: Labarin 'Sanadi'


Ku latsa alamar hoton da ke sama don sauraro:

A ci gaba da kawo muku karatun labaran da suka yi nasarar lashe gasar Hikayata ta bana, muna kan kawo muku labarai goma sha biyun da alkalan gasar suka ce sun cancanci yabo.

A wannan mako dai za mu kawo muku labarin “Sanadi” ne, na Asma’u Abdallah Ibrahim, Azhari Murabba Khamsa, Khartoum, Sudan, wanda Aisha Shariff Baffa ta karanta.

Bayani kan aikin hukumar zabe mai zaman kanta ta Nigeria


INECHakkin mallakar hoto
Getty Images

Ranar Juma’a ce ta kasance saura shekara guda cif a gudanar da zaben shugaban kasar Najeriya, idan komai ya tafi daidai kamar yadda Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta kasar, INEC, ta tsara.

A farkon watan Janairun bana ne dai hukumar ta INEC ta fitar da jadawalin zabukan shekara ta 2019.

Majalisun dokoki na kasar dai sun yi wa dokar zabe kwaskwarima ta yadda za a sauya jerin zabubbukan, amma sai shugaban kasa ya rattaba mata hannu kafin ta fara aiki.

Daga yanzu zuwa lokacin, za mu rika kawo muku makala akai-akai game da wasu batutuwan da suka shafi zabe a Najeriya.

A wannan mako mun fara ne da jin ko menene aikin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa?

Ga bayanin wani kwamishina a hukumar INEC Malam Mohammed Haruna:

Amsa: Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ita ce wacce take zaune a Abuja take kuma gudanar da zabe ba tare da karbar umarni daga wajen kowa ba.

Tambaya: Wadanne irin ayyuka take yi ba ya ga gudanar da zabe?

Amsa: Babban aikin da muke yi shi ne na gudanar da zabe, kuma akwai yi wa masu zabe rijista, mu ne kuma muke yi wa jam’iyyu rijista. Saboda kundin tsarin mulkin kasar ya ce ba za ka gudanar da zabe ba sai kana mamba na wata jam’iyya.

Mu muke rijistar ‘yan takara da jam’iyyu mu kuma gudanar da dukkan zabuka ban da na kananan hukumomi.

Tambaya: Idan aka gudanar da zabe aka kuma samu rikici tsakanin jam’iyya da jam’iyya, akwai inda hukumar zabe ke shiga don sasantawa ko kafa hujja?

Amsa: Kwarai da gaske. Ya danganta da irin rigimar, kotu na iya kiranmu tun da mu muke yi wa ‘yan takara rijista. Kuma idan za su tsayar da masu takara muna zuwa sanya ido. Idan kotu ta bukaci jin ta bakinmu, mu kuma za mu bayar da rahotonmu.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Tambaya: Ta wacce hanya INEC ke samun kudadenta don shirya zabuka?

Amsa: Kundin tsarin mulkin kasa ya yi tanadin cewa kai tsaye za a ciro kudin shirya zabuka daga asusun gwamnatin tarayya, in dai mun kai kasafin kudi majalisa ta amince, shugaban kasa ya sa hannu, to kai tsaye za a ba mu kudin daga asusun gwamnati.

Mene ne bambancin hukumar zabe ta kasa da ta jiha?

Amsa: Hukumar zabe ta kasa ce ke tsara zabukan shiga majalisar wakilai da ta dattijai da na majalisar dokokin jihohi da na gwamnoni da na shugaban kasa. Amma zabukan kananan hukumomi kamar na Ciyaman da Kansiloli, to hukumar zaben jiha ce ke yi.

Da a lokacin mulkin soja, hukumar zabe ta kasa ce ke yi, amma da aka sake kundin tsarin mulki na 1999 sai aka bai wa jihohi wannan damar.

Tambaya: A misali yanzu idan hukumar zabe ta jiha ta shirya zabe, ake kuma zargin ba a yi wa wani bangare adalci ba, shin hukumar zabe ta kasa tana shiga cikin maganar?

Amsa: A’a, ba ruwanmu da wannan. Ba ruwanmu da zaben da hukumar zabe ta jihohi ke yi. Sai dai a wasu lokutan mu na taimaka musu da kayayyakin gudanar da zabe. Majalisar jihohi ne ke tsara musu dokoki. Mu kuwa majalisar wakilan tarayya da ta dattijai ke tsara mana dokokinmu.

Tambaya: Ko hukumar zabe na da wasu hanyoyin samun tallafi baya ga gwamnatin tarayya?

Eh hukumomi kamar na Majalisar Dinkin Duniya irin su UNDP da Commonwealth kan taimaka amma ba wai yta hanyar ba mu kudi ba. Su kan taimaka mana da masaukai da kudin zirga-zirga a lokutan da gudanar da bayar da horo ko wasu taruka. Ba Najeriya kadai suke wa haka ba su na yi wa kasashe da dama. Amma ba ma barin su shigo cikin abun da ya shafi harkar gudanar da zabe.

Sai ku dinga kasancewa da mu a rediyo duk bayan mako biyu da don jin bayanai game da hukumar zabe ta kasa da shirin zaben 2018.

Sannan kuna iya karanta bayanan a shafinmu na www.bbchausa.com, kuma za ku iya aiko da tambayoyinku kan abin da kuke son sani game da batutuwan.

Jirgi ya yi hatsari da fasinja 60 a Iran


Iran Tehran Semirom map

Kafafen watsa labarai sun ruwaito cewa wani jirgin saman fasinja dauke da mutum sama da 60 ya yi hatsari a yankin da ke cike da tsaunuka na kasar Iran.

Jirgin ya fado ne a yankin Zagros mai cike da tsaunuka a lardin Isfahan a lokacin da yake kan hanyarsa daga Tehran Yasuj da ke kudu maso yammacin kasar, in ji wasu rahotanni.

“An sanya dukkan hukumomin bayar da agajin gaggawa cikin shirin ko-ta-kwana,” in ji wani jami’in hukumar bayar da agaji.

Rashin yanayi mai kyau ya hana wani jirgi mai sukar ungulu da ke kai agajin gaggawa zuwa wurin da lamarin ya faru.

Har yanzu dai hukumomi ba su ce komai kan mutanen da lamarin ya hada da su ba.

An yi amannar cewas jirgin samfurin ATR 72-500 na kamfanin jiragen saman Aseman ne.

Rahotanni sun ce fasinjoji 60 a cikinsa, da matukan jirgi biyu da kuma ma’aikatansa biyu.

Trump ya soki hukumar FBI saboda gazawa kan kisan da aka yi a Amurka


A young girl sits at a temporary memorial in Parkland, Florida. Photo: 17 February 2018Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Harin shi ne mafi muni da aka kai a wata makaranta a Amurka tun shekarar 2012

Shugaban na Amurka Donald Trump ya caccaki hukumar binciken laifuka, FBI saboda rashin gano alamun da suka nuna cewa za a kai hari a wata makarantar Florida ranar Laraba.

Hukumar binciken laifuka, FBI ta “buge tana bata lokaci wurin bincike domin ta gano ko Russia ta taimaka min” wurin lashe zaben 2016, in ji Mr Trump a wani sakon Twitter da ya wallafa.

“Babu wata alaka tsakanina da su. Ya kamata ku je ku yi aikinku da ya kamata domin mu rika alfahari da ku.”

FBI ta amince cewa ta gaza wurin daukar mataki bayan an gaya mata cewa mutumin da ake zargi ya harbe ‘yan makarantar Parkland lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum 17, Nikolas Cruz, na shirin kai harin.

Harin shi ne mafi muni da aka kai a wata makaranta a Amurka tun shekarar 2012 kuma ya kara taso da batun nan na takaita mallakar makamai.

Tunda fari dai, daliban da suka tsira daga harin na Florida sun bukaci a dauki tsauraran matakai wurin hana mutane mallakar bindigogi sannan suka soki shugaban kasar saboda karbar tallafin da ya yi daga kungiyar masu rajin ci gaba da mallakar makamai ta kasar, lokacin da yake yakin neman zabe.

Hakkin mallakar hoto
Joe Raedle

Image caption

Harin shi ne mafi muni da aka kai a wata makaranta a Amurka tun shekarar 2012

Hotunan abubuwan da suka faru a Afirka a makon jiya


Mun zabo muku fitattun hotunan abubuwan da suka faru a nahiyar Afirka da ‘yan Afirka a wannan mako.

Invited guests watch the film "Black Panther" in 3D in Nairobi, Kenya, on February 14, 2018Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Wannan hoton wasu daga cikin mutanen da suka je kallon fim din Black Panther a gidan sinimar da ke Nairobi, babban birnin kasar Kenya ranar Laraba

Ghana's Akwasi Frimpong slows down at the end of the men's skeleton heat 1 during the Pyeongchang 2018 Winter Olympic Games, at the Olympic Sliding Centre on February 15, 2018 in PyeongchangHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Wani sun bayyana dan kasar Ghana Akwasi Frimpong a matsayin gwarzo bayan da ya shiga gasar Sululun tafi-da-ka a wajen gasar Olympics ta hunturu da aka yi a Korea Ta Kudu ranar Alhamis. Shi ne ya zo na karshe a gasar.

Simidele Adeagbo of Nigeria starts her women's skeleton training session at the Olympic Sliding Centre, during the Pyeongchang 2018 Winter Olympic Games in Pyeongchang, South Korea on February 14, 2018.Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Nan kuma dan kasar Najeriya ne Simidele Adeagbo yake yin atisaye domin fafatawa a gasar Sululun tafi-da-ka , inda mutum ke dirawa da ka a gudun mil 85 cikin awa daya.

Sabrina Simader competes in the Pyeongchang 2018 Winter Olympics Women's Giant Slalom Yongpyong Alpine Centre on 15 February 2018.Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Ranar Alhamis, ‘yar kasar Kenya Sabrina Simader ta fafata a wasan zamiyar kankara ta gociya. Ita ce ta zo ta 59.

A nail artist fixes client's nail on Valentine's Day at Wuse market in Abuja, Nigeria 14 February 2018Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

A Abuja, babban birnin Najeriya, shagon da ake yankan farce da gyara jiki ya cika makil da masu hulda ranar 14 ga wata, lokacin da aka yi bikin ranar masoya.

Bouquets of roses are for sale for Valentine's Day at a flower shop in Nairobi on February 14, 2018.Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Idan har ka sayi fure domin tunawa da ranar masoya ta duniya, Kenya cikin kasashen da suka fi fitar da irin wadannan furannin, kamar wadannan da ke Nairobi, babban birnin kasar.

Supporters of Bekele Gerba, secretary general of the Oromo Federalist Congress (OFC), chant slogans to celebrate Gerba's release from prison, in Adama, Oromia Region, EthiopiaHakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Ranar Laraba, magoya bayan jagoran ‘yan hamayyar Ethiopia, Bekele Gerba, sun yi gangami domin murnar sako shi daga gidan yari.

Supporters of Bekele Gerba, secretary general of the Oromo Federalist Congress (OFC), chant slogans to celebrate Gerba's release from prison, in Adama, Oromia Region, Ethiopia February 14, 2018Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Ranar Laraba ne aka shiga kwana na uku na zanga-zangar kyamar gwamnati da ake yi a Oromia, yanki mafi girma a kasar Ethiopia, inda aka bukaci a saki manyan ‘yan siyasa da ‘yan jaridar da ke dauke a kurkuku.

South Africa's President Jacob Zuma looks down as he speaks at the Union Buildings in Pretoria, South Africa, February 14, 2018.Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Da yammacin ranar Laraba ne Shugaba Jacob Zuma na Afirka Ta Kudu ya bayar da sanarwar sauka daga mulki bayan ya sha matsin lamba…

Cyril Ramaphosa arrives at the parliament, in Cape Town, South Africa, 15 February 2018.Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

… washegari ne aka sanar cewa mataimakinsa Cyril Ramaphosane sabon shugaban kasar Afirka Ta Kudu a zaman da majalisar dokoki ta yi cike da raha da dariya da kuma wakoki.

A member of Zimbabwe's opposition party "Movement for Democratic Change" (MDC) stands outside Harvest House, the party's headquarters, in Harare on 15 February 15, 2018.Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Ranar Alhamis ‘yan Zimbabwe suka taru a bakin ofishin jagoran ‘yan hamayyar kasar Morgan Tsvangirai domin nuna jajensu bayan an sanar da mutuwarsa sakamakon cutar daji ta hanji. Ya mutu yana da shekara 65.

Hotunan na AFP, Reuters, da kuma Getty Images ne.

Isra'ila ta kai hari a Gaza


Fashewar ta faru ne kusa da wata katanga da ke zirin GazaHakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Fashewar ta faru ne kusa da wata katanga da ke zirin Gaza

Isra’ila ta kaddamar da munanan hare-hare ta sama a wuraren da ‘yan kungiyar Hamas ke zaune a zirin gaza, a matsayin martani game da harin bam da aka kai kan sojojinta.

Ta ce harin bam din ya raunata sojojinta su 4.

Rundunar sojin Isra;ila ta ce ta kai hari wurare 18 da ‘yan kungiyar din suke zaune cikin har da waje da suke ajiye makamai da kuma hanyar karkashin kasa da ke kan iyaka da Isra’ila.

Kazalika wata tankar Isra’ilar ta bude wuta a wani waje da ‘yan kungiyar Hamas din ke zaune.

Lamarin dai ya hallaka Falasdinawa biyu .

Sai dai sojojin Israilar sun ce mutanen na cikin wani gungun Falasdinu da suka doshi kan iyakar kasar kuma akwai alamar tambaya game da manufarsu.

Likitoci a Gaza sun ce an raunata Palasdinawa biyu, yayinda ba a ga wasu uku ba a hare haren da Israilar ta kai.

Real Madrid ta kusan cin kwallo 6,000 a La Liga


Real MadridHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Real Madrid za ta ziyarci Real Betis a ranar Lahadi a wasan mako na 24 a La Liga

Kungiyar Real Madrid ta kusa cin kwallo 6,000 a tarihin gasar cin kofin La Ligar Spaniya, bayan da ta ci 5,997 kawo yanzu.

Watakila kungiyar ta cika she guda ukun ko ta haura ko kuma ta kasa a ranar Lahadi a gasar mako na 24 da za ta ziyarci Real Betis.

An fara buga gasar cin kofin Spaniya a 1928/29, inda Real Madrid ta ci kwallon farko ta hannun Jaime Lazcano a karawar da ta yi da CE Europa.

A fafatawar ce Real ta ci kwallo 5-0 kuma Lazcano ne ya ci hudu rigis, tun daga nan sai da Madrid ta yi shekara 22 kafin ta saka sunanta cikin tarihin gasar La Liga.

Domin sai a ranar 5 ga watan Nuwambar 1950 Real ta ci kwallo na 1,000 ta hannun Manuel Fernandez Fernandez a karawar da ta doke Athletic Club 5-2 a San Mames.

Paco Gento ne ya ci kwallo na 2,000 a wasan da Real ta doke Pontevedra 3-1 a Santiago Bernabeu, a ranar 20 ga watan Janairun 1982, Real ta ci na 3,000 ta hannun Juan Gomez a gumurzu da Salamanca.

Ivan Zamorano ne ya ci kwallo na 4,000 shi ne na biyun da ya ci a fafatawar da suka doke Real Valladolid 5-0, yayin da Raul Gonzalez ne ya ci wa Real Madrid kwallo na 4,500.

Guti ne ya ci na 5,000 a ranar 14 ga watan Satumbar 2008, a wasan da Real ta doke Numancia 4-3 a Bernabeu.

A kakar 2012/13 Real Madrid ta hada kwallo na 5,500 ta hannun Luka Modric a wasa da Malaga.

Kungiyar da magoya bayanta na lissafin dan wasan da zai ci wa Real Madrid kwallo na 6,000 a tarihi.

Ko kun san matar da ta kammala digirin digirgir a cikin watanni uku?


Grace Mugabe, ta samu takardar kammala karatun digirin digirgir a cikin watanni ukuHakkin mallakar hoto
EPA

Image caption

Grace Mugabe, ta samu takardar kammala karatun digirin digirgir a cikin watanni uku

Jami’an tsaro sun cafke mataimakin shugaban wata jami’a a kasar Zimbabwe Levi Nyagura, bisa zarginsa da hannu a dambarwar da ta kunnu kai kan ba wa matar tsohon shugaban kasar Grace Mugabe, takardar shaidar kammala karatun digirin digirgir.

An dai ba ta wannan digiri ne alhali watanni kalilan ta yi ta na karatu, kuma sai a watan da ya gabata ne aka wallafa kundin binciken da ta yi, a dai-dai lokacin da ake kirayen a karbe digirin ba ta cancance shi ba.

Abin da ba a bayyana ba shi ne ko ita ma Misis Grace Mugaben, za a cafko ta don fuskantar tukumar.

Maimakon yadda aka san masu karatu mai daraja irin wanda aka bata da shafe shekara da shekaru kafin kammalawa da karbar sakamako, ita na ta ya kammala ne cikin dan takaitaccen lokaci.

Rashin adalci ne a zargi Grace da laifin Mugabe – ‘Yar Majalisa

‘Uwargidan shugaban kasa ta raba rigunan mama’

Wasu bayanai da suka kara fitowa ma shi ne, baki daya tun daga yin rijista a jami’ar da fara daukar karatu, da zana jarrabawa, da rubuta kundin bincike da ma ba ta takardar shaidar digirin digirgir din, lokacin da ta dauka bai wuce watanni biyu zuwa uku ba.

Ita dai Grace Mugabe, ta so ta gaji mijinta Robert Mugabe ne, a matsayin shugabar kasar Zimbabwe, amma hakar ta ba ta cimma ruwa ba inda a watan Nuwambar bara sojin kasar suka hambarar da gwamnatinsa kamar yadda ‘yan kasar suka da de su na fata, yayin da ita kuma ta tsere daga kasar tun ma kafin sojojin su kawo karshen gwamnatin mista Mugaben.

United ta kai zagayen gaba a kofin FA


Man UnitedHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

United tana ta biyu a kan teburin gasar Premier ta shekarar nan

Manchester United ta yi nasarar cin Huddersfield 2-0 a wasan zagaye na biyar a kofin FA da suka kara a ranar Asabar.

United ta ci kwallayen ta hannun Romelu Lukaku, wanda ya ci na farko a minti na biyar da fara tamaula, sannan ya kara na biyu bayan da aka dawo daga hutu.

Wannan ne wasa na uku da United ta buga da Huddesfield a bana, inda ta ci karawa biyu, Huddersfield ta ci daya.

Huddesfield ce ta fara doke United a wasan farko a gasar Premier da ci 2-1 a ranar 21 ga watan Oktoban 2017, United ta ci 2-0 a Old Trafford a ranar 3 ga watan Fabrairun 2018.

Barcelona ta buga La Liga 24 a jere ba a doke ta ba


BarcelonaHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Barcelana ta ci wasa 19 ta yi canjaras biyar ta kuma ci kwallo 61 aka zura mata 11 a raga

Barcelona ta yi nasarar cin Eibar 2-0 a wasan mako na 24 a gasar cin kofin La Liga da suka kara a ranar Asabar.

Luis Suarez ne ya ci wa Barcelona kwallon a minti na 16 da fara wasa, kuma na 17 da ya ci a kakar shekarar nan, sannan Jordi Alba ya ci na biyu saura minti biyu a tashi daga wasan.

Eibar ta karasa fafatawar da ‘yan wasa 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Fabian Orellana jan kati, shi ma kocin kungiyar, Jose Luis Mendilibar an koreshi daga bakin filin wasa, bayan da ya harzuka sakamakon korar Orellana da aka yi.

Wannan ne karo na shida da aka kori Orellana a gasar La Liga, uku daga ciki a lokacin karawa da Barcelona.

Barcelon ta yi wasa 24 a kakar La Liga ta bana ta ci 19 ta yi kunnen doki karo biyar, ta kuma ci kwallo 61 aka zura mata 11 ta hada maki 62.

Girona za ta ziyarci Barcelona a wasan mako na 25 a ranar 24 ga watan Fabrairu.

Real Madrid za ta yi wasa hudu a kwana 10


Real MadridHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Real tana ta hudu a kan teburin La Liga, za kuma ta ziyarci Real Betis a ranar Lahadi

Real Madrid za ta buga wasan gasar La Liga hudu a kwana 10, bayan da kungiyar take ta hudu a kan teburin bana.

A ranar Laraba Real ta ci Paris St Germain 3-1 a wasan farko na zagaye na biyu a gasar cin kofin zakarun Turai, za kuma ta mai da hankali kan La Liga domin ta samu gurbin shiga gasar badi.

Real za ta fara ziyartar Real Betis a wasan mako na 24 a ranar Lahadi, kungiyar da ta doke Madrid 1-0 a watan Satumba a Santiago Bernabeu.

Kwana uku tsakani Real za ta ziyarci Leganes a wasan mako na 25, daga nan Madrid ta karbi bakuncin Alaves a Bernabeu a ranar 24 ga watan Fabrairu a wasan mako na 26.

Wasa na hudu cikin kwana 10 da Madrid za ta yi shi ne na mako 27, wanda za ta ziyarci Espanyol, duk da cewar kila wasan Espanyol da Alaves na kasan teburi, amma za ta yi gumurzu a fafatawa da Betis da Leganes domin suna kan ganiyarsu.

Daga nan ne Real za ta yi hutun mako daya sannan ta karbi bakuncin Getafe a Bernabeu, kwanaki uku tsakani ta ziyarci Faransa domin karawa da PSG a wasa na biyu a gasar cin kofin zakarun Turai.

Talauci ya sa mata na bayar da hayar mahaifarsu a Ukraine


Wata likita ta na daukar hoton cikin wta mai juna biyu, dan gano kwanviyar jariri, ko sanin jinsi ko kuma gano wata matsala a wani asibiti mai suna Ilaya a Ukraine

Presentational white space

Kasar da ke cikin kasashen da suka fi talauci a nahiyar Turai wato Ukraine, ta tasamma zama tudun mun tsira ga ma’auratan da ba za su iya haihuwa ba ko ba sa haihuwa baki daya.

A kan biya matan kasar kudade masu yawa su taimakawa matan da ba sa haihuwa wajen daukar ciki, su kuma biya su da zarar ta haihu lafiya sun karbe jaririn da aka samu.

Makudan kudaden da ake biya ne dai su ka janyo hankalin mata matasa don shiga harkar. Sai dai abin da ake nuna damuwa shi ne ko mecece makomar matan masu daukar cikin?

Shekarun Ana 18, a lokacin da ta samu labarin daukarwa wasu daban ciki da haife musu jariri a tashar talabijin.

Ba ta jima da kammala karatun sakandare ba, kuma ta fara tunanin samun aiki a wani Otal a dan karamin garin da suke zaune da iyayenta gabashin Ukraine, yankin da masu yawon bude ido ke zuwa don shakatawa.

Aikin Otal din dai dala 200 za a din ga ba ta a kowanne wata, amma daga bisani ta gano idan ta dauki ciki ta kuma haife shi za ta samu akalla dala 20,000.

Duk da cewa iyayen Ana ba matalauta ba ne, amma dai ma su karamin karfi ne don mahaifiyarta akawu ce kuma ta na taimaka mata kwarai da gaske.

Amma duk da hakan batun daukar cikin da haihuwa a kuma biya makudan kudade ya dauki hankalinta, ”Na zabi yin hakan ne, don na samu abin kaina, da kuma tallafawa iyayena don rage wahalhalun da ke kansu, da gyara gidanmu kai har da siyan motar hawa” in ji Ana, duk da cewa tsorace ta ke magana, kuma ba ita ce ta farko da za ta fara yin hakan ba a cikin Ukraine.

Na’urarku na da matsalar sauraren sauti

Ana mai shekara 23, ta ce matan da ke daukar ciki ta wannan hanya yana da matukar muhimmanci su yi taka tsantsan

Ma’aurata daga kasashen waje, na tururuwa zuwa wannan yankin tun a shekarar 2015, a lokacin da matan yankin Asia suka fara daina wannan kasuwanci bayan hukumomi sun fara samun rahotannin aikata ba daidai ba.

Masu zuwa kasashe kamar Indiya, da Nepal, da Thailand da suka haramta yin hakan sun fara karkata zuwa Ukraine da kasuwar ta ke haskawa a wannan lokacin.

“Mu na samun ma’aurata da dama daga Turai da ba su taba haihuwa ba, kuma su na tsananin bukatar ‘ya’ya,” in ji Ana.

A lokacin da ta ke shekara 21, bayan daukar lokaci tana aiki a wani Otal, daga bisani Ana ta bar aikin Otal ta rungumi daukarwa ma’auratan da ke bukatar ‘ya’ya ciki.

Kafin ta fara harkar, sai da ta haifi ‘yarta don tabbatar da cewa tana haihuwa.

A karkashin dokokin kasar Ukraine sai an tabbatar da matar da za ta dauki cikin ta taba haihuwa, ko dai danta na kashin kai ko kuma ta taba haifawa wani.

Idan kuma mace na da danta, akwai yiwuwar ba za ki yadda ki shaku da dan da kika haifawa wasu a lokacin da za a dauke shi ba.

Image caption

Ana tana fatan saya ‘yarta gida a garinsu Kamyanets-Podilskyi

Tafiya mai tsawo

Ana ta fara mayar da hankali wajen duba intanet inda a nan ne ake samun masu neman haihuwa da asibitocu suke bayar da cigiya.

Ba a dade ba ta yi tafiya zuwa Kiev babban birnin kasar domin a duba lafiyarta. Ta sa hannu a wani kwantiragi da wasu ma’aurata a Slovenia wadanda ba su taba samun dan kansu ba.

Ana ta yi sa’a an dasa mata kwan haihuwa a mahaifarta, inda a karon farko ta dauki ciki don haife wa wasu da.

Amma a lokacin ne ta fara fuskantar wahalhalun. Ta ce kulawar da ake ba ta a asibitin ba ta dore ba.

A cewarta, wasu daga cikin yaran da aka dasa din na dauke da wasu nau’uka na rashin lafiya da ba a tantance da kyau ba ko kuma ba a dauki matakin warkarwa a kan loakaci ba.

Ta wallafa korafe-korafenta a intanet don gargadin sauran mata, amma sai asibitin suka karyata ta, kuma sai ta ji tsoron bayyana sunansu.

Jaririn da ta haifa lafiyayye ne amma kuma ta kasance cikin taka-tsan-tsan saboda abun da ya faru. Amma duk da haka ta amince ta kara yin wannan aiki, sai dai wannan karon wasu ma’aurata ‘yan aksar Japan ne suka yi hayarta don haifa musu da.

Sun damka al’amuran da ya shafi batun a hannun wani lauya a Kiev, kuma da alama ba za ta taba ganin su a zahiri ba.

Kuma ta kasance mai taka tsan-tsan wajen zabar asibitin da za su kula da ita a wannan karon, amma idan komai ya tafi yadda aka shirya, za ta haifi ‘ya’ya uku a lokacin da take da shekara 24 – daya kanta ta haifarwa, biyu kuwa hayarta aka yi ta haifar wa wasu.

Karuwa hayar mata don su haifi yara

An samu karuwar yawan hayar mata don su haifar wa wasu yara a Ukraine da kashi 1000% cikin shekara biyu da suka gabata kawai, in ji Sam Everingham na cibiyar agaji ta Families Through Surrogacy, da ke wadda ke bai wa iyayen da ke son haihuwa shawara.

Ya kara da cewa, “Ukraine ta samu kanta a yanayin da ta zamo cikin kasashe kalilan da aka mayar da harkar hayar mata don su haifar wa wasu ‘ya’ya tamkar harkar yawon bude ido.”

Bayan kasancewar yin hakan halal ne a Ukraine, saukakan dokokin kasar na kara jawo hankalin mutane

Mista Everingham ya kara da cewa, “Mun ga misalai da dama a Ukraine inda wakilan da ake damkawa ragamar wannan harka suke cutar da matan da ake dauka haya wajen kin biyansu hakkinsu, idan har ba su cika ka’idojin da suka shimfida musu ba, kamar idan suka yi bari.”

Image caption

Matan da ke goyon dan tayin na yawan zuwa birnin Kiev don duba lafiyarsu

Yaya goyon dan tayi yake aiki a Ukraine?

 • Ana yin sa ne ga ma’auratan da suke da shaidar tabbacin cewa matar ba za ta iya goyon ciki ba, ko kuma
 • Dole ne daya daga cikin iyayen ya kasance ita ke da kwan dan tayin da za a yi hadin da shi; ana amfani da kwan da wasu ke bayar da kyautarsa
 • Farashin ya bambanta, amma ya kan kama daga dala dubu 30 zuwa dubu 40 akasari
 • Iyayen da za su biya kudin suna da takardar shaidar haihuwa ta Ukraine, amma matar da ta yi goyon dan tayin har ta haife shi ba ta da iznin mallakar jaririn
 • An kiyasta cewa kusan masu goyon dan tayi 500 ake samu duk shekara amma dai ba a cika samun cikakkun bayanai ba
 • An amince da irin wannan goyon dan tayi na kasuwanci a Amurka Georgia da Rahsa. Ana yin wannan tsarin a Kenya ma da Laos amma kuma babu dokar da ta haramta ko halalta haka a kasashen.

Image caption

Wannan jaririn ma hayar wata aka yi ta yi goyon cikinsa ta haifarwa wasu

Pogba ba zai buga karawa da Huddersfield ba


Man UnitedHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

United ce za ta ziyarci Huddersfield a kofin FA wasan zagaye na biyar

Dan wasan Manchester United, Paul Pogba ba zai buga karawar da kungiyar za ta yi a kofin FA da Huddersfield a ranar Asabar, sakamakon rashin lafiya da yake fama.

United ta tame gurbin Pogba da dan wasan matasan kungiyarta, Ethan Hamilton mai shekara 19.

Shi kuwa Erik Bailly ya murmure, bayan jinyar wata uku da ya yi sakamakon aiki da likitoci suka yi masa a kafarsa.

Sai dai kuma Ander Herrera da Marcus Rashford ba za su buga fafatawar ba, sakamakon jinya da suke yi.

A ranar Asabar United ta fitar da sanarwar cewar Pogba ba zai samu damar buga wasan zagaye na biyar a gasar FA da Huddersfield ba.

Arsenal na son sayen Werner na RB Leipzig


ArsenalHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

The Sun ta ce Chelsea da Liverpool da Manchester United na son sayen Werner

Arsenal na son sayen dan wasan RB Leipzig, mai cin kwallo Timo Werner, mai shekara 21 dan kasar Jamus in ji jaridar The Sun.

Jaridar ta wallafa cewar Chelsea da Liverpool da Manchester United sun taya dan wasan kan fam miliyan 50, inda kungiyar Jamus bata sallamar ba.

Mail kuwa cewa ta yi Arsene Wenger na shirin daukar dan wasan Lyon mai wasan tsakiya, Nabil Fekir kuma shi ne na farko da zai fara kai wa Gunners, zai iya biyan fam miliyan 45 domin a dauki dan kwallon Faransa mai shekara 24.

Liverpool na bibiyar dan kwallon Tottenham, Victor Wanyama, bayan da Emre Can ba shi da makoma a Anfield in ji Mail.

The Sun ta ce aikin Alan Pardew na tangal-tangal, lokacin da ‘yan wasan West Brom hudu suka nemi gafara, bayan da aka sace taksi a wajen dakin abinci a Barcelona a ranar Alhamis.

Telegraph ta wallafa cewar kocin Manchester City, Pep Guardiola ya ce kungiyar bata aikata laifi ba a lokacin da ta kasa sayen dan wasan Leicester City, Riyad Mahrez a watan Janairu.

Manchester United na son sayen dan kwallon Nice, Jean Michael dan kasar Ivory Coast, wanda kunshin yarjejeniyarsa ya tanadi kudin sayar da shi fam miliyan 33 in ji Mail.

Obasanjo ya kai wa Jonathan ziyara


Cif Obasanjo ya sha caccakar Mr JonathanHakkin mallakar hoto
PDP

Image caption

Cif Obasanjo ya sha caccakar Mr Jonathan

Tsohon shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya kai wa tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan ziyara a gidansa da ke Otueke da ke kudu maso kudancin kasar.

Cif Obasanjo ya je jihar Bayelsa ne domin kaddamar da wasu ayyukan da gwamnatin jihar ta yi, a cewar jam’iyyar PDP da ke hamayya a kasar.

“Daga nan ne ya kai ziyara wurin Goodluck Jonathan a gidansa da ke Otuoke,” in ji PDP, a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter.

Mr Jonathan damai dakinsa ne suka tarbo tsohon shugaban kasar.

A baya dai, Obasajo ya soki Mr Jonathan saboda rashin iya gudanar da mulki a lokacin da yake shugabancin Najeriya, yana mai cewa Obasajo dai ya soki shugaba Goodluck Jonathan saboda rashin iya gudanar da mulki, yana mai cewa Mr Jonathan na so ya sake cin zaben kasar ko ana so ko ba a so idan ba haka ba kuwa zai jefa kasar cikin rikici.

Cif Obasanjo ya zama shugaban Najeriya sau biyu, kuma shi ne ya zabi shugaba Jonathan domin zama mataimakin marigayi shugaba Umaru ‘Yar Adua.

A watan jiya, Cif Obasanjo ya soki Shugaba Buhari saboda “rashin iya shugabanci” inda ya yi kira a gare shi da kada ya sake tsayawa takarar shugabancin kasar.

Ya kafa wata kungiyar siyasa da ya ce ita ce za ta iya ceto kasar daga kangin da take ciki.

Masu sharhi na gani tsohon shugaban gwano ne da ba ya jin warin jikinsa, suna masu cewa shi kansa bai iya mulki ba lokacin da ya yi shugabancin kasar.

Hakkin mallakar hoto
PDP

Image caption

Cif Obasanjo ya sha caccakar Mr Jonathan

An yanke wa mai fyade hukuncin kisa sau hudu a Pakistan


Zainab Ansari, who was murdered in Pakistan, aged sixHakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Fyaden da aka yi wa Zainab ya jawo tur daga dukkan Pakistan

Wata kotun Pakistan ta yanke hukuncin kisa sau hudu kan Imran Ali, dan shekara 24, saboda samunsa da laifin fyade da kisan wata yarinya ‘yar shekara shida a watan jiya.

An tsinci gawar Zainab Ansari a cikin bola a birnin Kasur da ke kudancin Lahore ranar tara ga watan Janairu.

Kisan nata ya jawo Allawadai daga dukkan fadin kasar, inda mutane suka yi zanga-zanga saboda zargin ‘yan sanda da rashin daukar mataki.

Mutum biyu ne suka mutu sanadin zanga-zangar.

Mahaifin yarinyar ya halarci zaman kotun, wanda aka yi shi cike da jami’an tsaro.

An zargi mutumin da ya kashe Zainab da hannu a wasu kashe-kashe da cin zarafin kananan yara mata a yankinsu.

Mutane da dama ne suka bayar da shaidar da ke nuna cewa yana da laifi, kuma bincike kan kwayoyin halittar sun nuna cewa shi ne ya aikata laifin.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

An zargi Ali da aikata laifukan kan kananan yara

Hakkin mallakar hoto
CCTV images

Image caption

An nuna hotunan da aka dauka da kyamarar sirri wadanda suka nadi yadda ake jan Zainab

Lauyan da ke kare Ali ya janye daga shari’ar bayan da wanda ake zargin ya ce ya aikata laifin.

An yanke masa hukuncin kisa saboda sacewa da yi wa yarinyar fyade da kuma kashe ta, da aikata ta’addanci da kuma yin luwadi, sannan an ci shi tara.

Wani shafin da ke bayar da labarai na intanet, Dawn, ya ce Ali yana da mako biyu da zai iya daukaka kara kan hukuncin da aka yi masa.

An matsa wa ‘yan sanda lamba sosai domin su gano mutumin da ya kashe Zainab da sauran yaran.

Mahaifan Zainab sun ce ‘yan sanda ba su dauki mataki kan batun ba a kwana biyar na farko da aukuwar lamarin.

Ranar 23 ga watan Janairu ne aka kama Ali.

'Yan kunar bakin wake sun kashe mutum 17 a Konduga


'Yan kunar bakin wakeHakkin mallakar hoto
Getty Images

Wasu ‘yan kunar bakin wake sun kai hari a Konduga da ke jihar Borno ta arewa maso gabashin Najeriya.

Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Satomi Ahmed ya shaida wa BBC cewa mutum 19 ne suka mutu, ciki har da ‘yan kunar bakin waken biyu.

A cewarsa, mutum sama da hamsin ne suka jikkata sakamakon harin, wanda aka kai a wata kasuwa da ke garin na Konduga, kuma tuni aka garzaya da su asibiti.

Ganau sun ce harin ya yi matukar muni.

Babu wanda ya dauki alhakin kai harin, sai dai ya yi kama da irin wadanda kungiyar Boko Haram ke kai wa.

Hukumomi a Najeriya na cewa suna cin galaba a yakin da suke yi da Boko Haram, ko da yake kungiyar ta matsa kai hare-haren kunar bakin wake.

A farkon makon nan ne rundunar sojin kasar ta sha alwashin bayar da tukwuicin N3m ga duk wanda ya bayar da bayani kan yadda za a kama shugaban wani bangare na Boko Haram Abubakar Shekau.

Rundunar ta ce Shekau ya koma sa “kayan mata da hijabi” a kokarinsa na tserewa.

Rundunar sojin Najeriya ta sha yin ikirarin kama Abubakar Shekau amma daga bisani ya fito ya musanta.

Mahara sun kashe sama da mutum '1000 a Zamfara cikin shekara shida'


An kashe mutane 'babu adadi'Hakkin mallakar hoto
zamfara government

Kisan da mutanen da ake zargi barayin shanu ne suka yi wa wasu mutane a Zamfara da ke arewacin Najeriya ya kara yawan alkaluman mutanen da aka kashe a jihar cikin shekara biyar da suka wuce.

A farkon makon nan ne ‘yan bindigar da ake zargi barayin shanu ne suka kashe mutane 35 a harin da suka kai a kauyen Birane cikin karamar hukumar Zurmi.

Sai dai ba wannan ne karon farko da ake kai irin wadannan hare-hare ba.

Hukumomi sun ce suna daukar matakai kan batun, amma masu sharhi kan sha’anin tsaro da ma ‘yan kasar na ganin matakan da ake dauka ba su yi tasirin hana kai hare-haren ba.

A watan jiya dan majalisar dattawan da ke wakiltar jihar Zamfara Sanata Kabiru Marafa ya shaida wa BBC cewa masu satar shanu sun kashe kusan mutum 1400 a jihar ta Zamfara cikin shekara biyar.

Sai dai Kwamishinan kananan hukumomin jihar, Alhaji Bello Dankande, ya gaya wa BBC cewa kalaman dan majalisar ya yi na cike da kura kurai.

Ga wasu hare-haren da ake zargi barayin shanu sun kai a jihar ta Zamfara:

Yuni, 2012

Wasu mutane dauke bindigogi sun kashe mutane akalla 23 lokacin suka kai harin kan kauyukan Dangulbi da sabuwar kasuwa Guru da sanyin safiya.

Mutane bakwai ne suka jikkata bayan maharan da ake zargin ‘yan fashi da makami ne sun afkawa kauyukan.

Ana dai jin cewar harin na ramuwar gayya ne kan yadda aka ce ‘yan banga a kauyukan suna fatattakar ‘yan fashin da ke addabar yankunan, inda a wasu lokuttan suke karkashe su.

Yuni, 2013

Rahotanni daga jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya na cewa, fiye da mutane 40 ne aka kashe a garin Kizara da ke Karamar Hukumar Tsafe da ke Jihar ta Zamfara.

Hukumomi sun ce wasu mutane dauke da makamai da ake zargin ‘yan fashi ne ne suka kai harin.

Bayanai sun nuna cewa, daga cikin wadanda suka rasa rayukansu har da Basarake, da kuma babban limamin garin.

Kakakin gwamnatin jihar ta Zamfara ya tabbatar da aukuwar lamarin kuma ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar ta Zamfara na daga cikin wasu manyan jami’ai da suka ziyarci garin domin ganin irin abubuwan da suka auku.

Mazauna yankin sun ce harin yana kama da na ramuwar gayya.

Kauyuka a jihar ta Zamfara da wasu yankuna masu makwabtaka da su na fama da irin wadannan hare hare da ake dangantawa da wasu ‘yan fashi dake cewar suna daukar fansar kisan wasu ‘yan uwansu da aka kashe.

Hakkin mallakar hoto
PREMIUM TIMES

Image caption

Gwamna Abdul’aziz Yari ya ce suna bakin kokarinsu

Afrilu, 2014

Hukumomi sun ce ‘yan bindiga sun kashe fiye da mutum 120 a harin da su ka kai a kauyen ‘Yar-Galadima da ke jihar, sai dai mazauna kauyen sun ce adadin ya kai 150.

Hankulan jama’a ya sun tashi sosai a kauyen, inda mata suka gudu, sai maza kalilan suka rage.

Lamarin ya faru ne lokacin da manoma da wakilan kungiyoyin ‘yan banga, daga jihohin Katsina da Zamfara da Kebbi da kuma Kaduna ke wani taro kan yadda za su bullo ma hare-haren da a ke kai masu.

Yuli, 2014

Wasu da ake zargin Fulani ne sun kashe fiye da mutane 50 tare da jikkata wasu da dama a gundumar Gidandawa da ke karamar Hukumar Maradun.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun yi wa kauyen kawanya ne da misalin karfe biyar na asuba, kana suka bude wuta ga duk wanda suka gani a lokacin.

Yuli, 2015

Wasu ‘yan bindiga wadanda ake kyautata zaton barayin shanu ne sun farwa kauyen Ci-gama da ke karamar hukumar Birnin-Magaji a jihar Zamfara, a yammacin jiya Asabar a inda suka kashe mutane 13.

Wani wanda ya shaida al’amarin ya shaida wa BBC cewa ‘yan bindigar sun yi wa kauyen shigar farar dango suka kuma bude wuta akan jama’a.

Disamba, 2015

Wasu ‘yan bindiga sun afka wa kauyen Mashema na karamar hukumar Bungudu inda suka kashe mutane ashirin.

Mazauna yankin, wadanda suka tabbatarwa BBC da aukuwar lamarin, sun kara da cewa mutum daya ya samu raunuka a harin.

Fabrairu, 2016

Wasu mutane da ake zaton masu satar shanu ne suka kai hari a kauyen Kwana da ke jihar Zamfara inda suka kashe mutane 23.

Afrilu, 2016

Rahotanni daga jihar Zamfara a Nigeria na cewa, wasu mahara da ake zargin Fulani ne sun kashe mutum shida a ƙauyen ‘Yar-tsaba.

Wasu mazauna kauyen shun shaida wa BBC cewa lamarin ya faru ne bayan maharan – wadanda suka je kauyen a kan babura – sun buɗe wuta a kan mutanen lokacin da suke gyara gonakinsu.

Mayu, 2016

An kashe sama da mutum mutum goma ƙauyukan Madaɗa da Ruwan Tofa da ke ƙaramar hukumar Ɗan Sadau sakamakon harin da ‘yan bindiga suka kai.

Wani Basarake a yankin ya shaida mana cewa maharan sun kashe mutum bakwai a Madaɗa, yayin da suka kashe mutum uku a Ruwan Tofa, kana suka jikkata mutum biyu.

Maris, 2016

‘Yan bindigar da ake zargi masu satar shanu ne sun hallaka mutane da dama a harin da suka kai kauyen Fanteka da ke jihar.

Jami’an ‘yan sanda sun ce kimanin mutane tara ne aka kashe a harin, yayin da wasu mazauna yankin suka ce adadin wadanda aka hallaka ya zarta hakan.

Nuwamba, 2016

‘Yan bindiga sun sake kai hari a wasu kauyuka a karamar hukumar Zurmi, inda wasu rahotanni ke cewa sun kashe mutane kimanin 44.

Harin – wanda aka kai da daddare – ya faru ne kwana daya bayan an kashe wasu mutane tare da sace wasu da dama, a wani harin na daban da aka kai a kan wasu kauyuka a yankin.

Wasu rahotanni sun ce kimanin mutane dubu daya ne suka tsere daga kauyukan domin tsira da rayukansu.

Rahotannin sun ce ‘yan bindigar sun isa kauyukan Tubali da Daular Moriki ne a kan babura masu yawa, inda suka rika harbin kan-mai-uwa-da-wabi.

Lamarin ya faru ne kwanaki kadan bayan an yi garkuwa da sama da mutane 40 da suke kan hanyarsu ta zuwa cin kasuwa.

Nuwamba, 2017

Mutanen da ake zargi masu satar shanu da garkuwa da mutane don neman kudin fansa ne sun hallaka fiye da mutum 50 a garuruwan Faro da Kubi da Shinkafi.

Sarkin Shanun Shinkafi Dakta Sulaiman Shu’aibu ya shaida wa BBC cewa, cikin dare mutanen da ake zargin suka je wani kauye mai suna Tunga Kabau, suka kashe mata 25 da kuma maza tara.

Daga nan ne kuma suka bankawa kauyen wuta.

Bayan nan kuma sun nufi wani kauyen da ake cewa Mallabawa, nan ma suka kashe mutum 19.

“Gaskiya ya kamata gwamnatin jihar Zamfara ta sake damara wajen kawo karshen hare-haren da masu satar shanu ke kai wa wasu kauyukansu,” in ji Dakta Sha’aibu.

Su ma mazauna garin Faro da Kubi duk a jihar ta Zamfaran, sun ce kwana biyu sun dan samu sassaucin hare-haren ‘yan ta’adda da barayin shanu, da kuma dauki dai-dai da ake musu.

Amma kuma tun daga makon da ya gabata hare-haren sun sake dawowa, kamar yadda suka ce.

Wani mazaunin garin Faro ya shaida wa BBC, cewa barayin shanun sun yi mummunar barna da ta hada da asarar rayuka da kona musu amfanin gona.

An sake sanya dokar ta baci a Habasha


.

Mutane sun rika farinciki bayan da aka sako yan siyasa da ke tsare da su a gidan yariHakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Mutane sun rika farinciki bayan da aka sako yan siyasa da ke tsare a gidan yari

Gwamnatin Habasha ta ce ta sanya dokar ta baci ne domin dakile yawaitar zanga -zangar kin jin ganin gwamnati da ake yi a kasar.

Wannan shi ne karo na biyu da gwamnati za ta ayyana dokar ta baci domin magance matsalar tashe tashen hankula a kasar .

Sai dai sanarwar da gwamnatin kasar ta fitar, ba ta yi karin haske ba kan tsawon waa’adin dokar ta bacin ko kuma kaidojin da zaa yi amfani da su ya yin wannan lokaci.

Matakin na zuwa ne bayanda fira minisran kasar Hailemariam Desalegn ya yi shellar yin murabus sakamakon tashe -tsahen hankulan da ake fuskanta a kasar.

Nan bada jimawa ba Majalisar dokokin kasar za ta dawo daga hutun da taje domin ta amince da murabus dinsa, wanda tuni hadin gwiwar jam’iyyyu masu mulki suka mara ma baya.

Habasha dai ta shafe shekara uku tana fuskankar zanga zangar kin jinin gwamnati a yankunan da dama ciki har da Oromiya wanda shi ne yankin mafi girma a kasar.

Wasu daga cikin bukatunsu masu zanga zangar sun hada da aiwatar da sauye sauye a harkar siyasar kasar, da hakkin dan kasa wajan mallakar fili tare da sakin yan siyasa da ake tsare da su a gidan yari.

A makon daya gabata ne hukumomin kasar suka sako daruruwan ‘yan siyasa masu hammaya da gwamati da kuma wasu yan jarida

Sai dai duk da haka jama’a sun cigaba da yin zanga zanga.

A shekarar 2016 ne gwamnatin kasar ta ayyana dokar ta baci har na tsawon watani goma.

Adikon Zamani: Yadda masu ciki za su kula da kansu


Ku latsa alamar lasifikar da ke sama don sauraron cikakken shirin:

A wannan makon mun kawo muku ci gaban tattaunawar da muka fara ne da wata likitar mata a makon da ya gabata, kan rainon ciki da haihuwa.

Bakuwata a wannan makon ita ce wata likitar mata, wadda ita ma uwa ce, Dr Habiba Ibrahim.

Samun ciki na daya daga cikin abubuwa masu muhimmanci da kan samu mace a rayuwarta.

Abun farin ciki ne, amma wasu matan hakan kan zo musu da tarin matsaloli, kama daga amai da tashin zuciya da sauran ciwuka manya da kanana, a wasu lokutan ma har da ciwukan da kan yi barazanar tafiya da rayuwarsu.

Ni da likitar mun tattauna sosai kan yadda za a iya daukar matakan rage radadin halin da mata kan samu kansu a ciki lokacin rainon ciki.

Samun haihuwa abu ne mai matukar dadi a rayuwa, sai dai a arewacin Najeriya har yanzu ana fama da yawan mace-macen mata da jarirai a sanadin haihuwa, saboda rashin wadatacciyar kula da ba sa samu yayin rainon ciki, musamman ma a karkara.

Muna nukatar neman mafita ga wannan yanayi da mata ke shiga. Wani lokacin sai na ga kamar ba ma daukar yanayin ciki da haihuwa da muhimmanci, bayan kuwa mun san cewa magana ce ta ko a mutu ko a rayu.

Samun da ba abu ne na wasa ba, amma ina mamakin yadda bangaren lafiya ba ya mayar da hankali sosai wajen taimakawa masu ciki da jariran da ake haifa.

Yin awon ciki wanda ke da matukar muhimmanci ya zama kwalele ga mata marasa galihu.

A cewar likitoci, rashin isasshiyar kula na iya jawo wa uwaye da jarirai matsala ko da can gaba ne a rayuwarsu.

Alal misali, wani bincike ya gani cewa uwayen da ke samun isasshiyar kulawa yayin da suke da ciki, sun fi haifar yara masu cikakkiyar lafiya.

Yadda Boko Haram da talauci suka 'wawure' kudin JAMB


kudaden Jamb

Hukumar da ke shirya jarrabawar shiga jami’a a Najeriya (JAMB), ta ce ta kama wasu jami’anta da dama da hannu a almundaha da kudaden hukumar a jihohi daban-daban, tun daga 2015 zuwa watan Agustar 2016.

Mai magana da yawun hukumar Fabian Benjamin, ya shaida wa BBC cewa hukumar ta gano hakan ne sakamakon wani kwamiti da ta kafa tun bayan zamowar Farfesa Ishaq Oleyede shugabanta, bayan ya gano cewa ana tafka badakala wajen sayar da katin yin rijistar jarrabawar wato Scratch Card.

Tana binciken miliyoyoin kudin da aka samu ne daga katin duba sakamakon jarabawar da dalibai suka dauka daga shekarar 2015 zuwa 2016.

Mista Benjamin ya ce wannan dalili ne ya sa aka kafa kwamitin bincike don gano irin badakalar da aka yi ta yi a hukumar don dakatar da faruwar hakan da kuma daukar matakan da suka dace.

A jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya, an samu babban jami’in hukumar, Sanusi Atose, da hannu a salwantar da naira 613,000, wanda ya ce yaki da kungiyar Boko Haram a yankin ne ya jawo.

A lokacin da Mista Atose yake ba da ba’asi ya ce “tashin hankalin Boko Haram ne ya sa bai san inda kudin suke ba.”

Jami’in ya ce takardun banki da rasitan duk sun lalace sanadiyyar hare-haren kungiyar, inda ya ce hakan ya sa ba shi da wata shaidar lissafe-lissafen kudaden da aka samu.

Sai dai shugaban hukumar Farfesa Oleyede ya yi watsi da hanzarinsa, inda ya ce wani yunkuri ne kawai na zamba.

“Ka je ka biya gwamnati kudinta nan da mako daya, idan kuma ba haka ba kana cikin matsala,” in ji shugaban kwamitin binciken.

Hakazalika, babban jami’in hukumar a jihar Kogi Daniel Agbor, ya ce ya “kashe naira miliyan bakwai wajen taimakawa wadansu ma’aikata wadanda talauci ya yi wa kanta.”

Har ila yau jami’in ya ce wadansu daga cikin katuna duba jarabawar da aka aika jihar wadansu mutane da ba a san ko su waye ba sun sace su.

“Halin da ake ciki a ofisoshinmu shi ne akwai talauci kuma akwai kudi a tare da mu,” in ji babban jami’in hukumar yayin da yake ba da ba’asi a gaban kwamitin.

Mista Agbor ya ce “mutum yana bukatar taimakon Ubangiji don Ya tsare shi daga yin sata saboda kudi na sauya mutum. Mun yi aron kudin ne kuma ba ni kadai ba ne, zan ba da sunayen duk wani da yake da hannu a wannan zambar.”

Babban jami’in hukumar a jihar Nasarawa Labaran Tanko shi ma cewa ya yi naira miliyan 23 na hukumar sun salwanta a hannunsa ne “bayan motarsa ta kama da wuta.”

Haka dai manyan jami’an hukumar na jihohin Kano da Gombe da Edo da Ondo da sauransu suka kasa yin bayanin yadda suka yi da miliyoyin kudin hukumar daya bayan daya.

Wannan batun ya fara mamaye kafafen yada labarai a fadin Najeriya ne bayan wata jami’ar hukumar a jihar Benue, Philomena Chieshe, ta yi ikirarin cewa wani maciji ya hadiye naira miliyan 36 na hukumar.

Hakkin mallakar hoto
EFCC

Image caption

An sha kama kudade a wurare daban-daban a Najeriya

Kuma tun bayan haka ne ake ci gaba da samun bayanai masu daure kai daga jami’an hukumar wadanda ake zargi da aikata zamba.

Hukumar ta dakatar da dukkan jami’an hukumar da ake zargi da almundahanar kuma ta mika wa ‘yan sanda batun don fara bincike kan al’amarin, kamar yadda mai magana da yawun hukumar Fabian Benjamin ya tabbatar wa BBC.

EFCC ta kama maƙudan kuɗi a Lagos

Da gaske ne EFCC ta gano kudi a makabarta?

Hakazalika ya ce hukumar ta rubuta rahoto kan wadanda ake zargin kuma ta mika shi ga ma’aitakar ilimi.

“Da zarar ta amince to za mu dauki matakan da suka dace kan wadanda ake zargin kamar yadda dokokin aikin gwamnati suka tanada,” in ji shi.

Cin hanci da rashawa da kuma almundahana da kudin gwamnati dai ya zama tamkar ruwan dare a Najeriya, sai dai tun bayan hawan Shugaba Muhammadu Buhari mulki ya fara yaki da wannan dabi’a kamar yadda ya yi alkawari lokacin neman zabe.

A yanzu dai ba za a iya cewa an daina cin hanci baki daya ba a Najeriya, amma akwai alamun cewa ana samun nasara a yaki da dabi’ar wacce Shugaba Buharin ke yi, ta hanyar bankado duk wanda aka samu da laifin.

Hakkin mallakar hoto
EFCC

Image caption

A bara ma an tseguntawa hukumar EFCC cewa an gano kudi a makabarta

Za a bada tukwicin kwai ga ma'aikatan da ke zuwa aikin da wuri


Za a ba wa ma'aikacin da ke zuwa aiki da wuri tukwicin kwai a VenezuelaHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Za a ba wa ma’aikacin da ke zuwa aiki da wuri tukwicin kwai a Venezuela

Wani kamfani da ke daukar hayar masu gadi a Venezuela, ya yi alkawarin bayar da tukwicin kwai 144 a duk wata ga ma’aikatan da ke shiga mai kyau da kuma zuwa aiki a kan lokaci.

Kasar Venezuela dai ita ce kasar da tafi fama da matsalar hahhawa da tashi farashin kayayyaki a duniya, kuma ta shafe shekaru tana fama da kanfar abinci da magunguna.

Trump ya yi barazanar daukar matakin soji kan Venezuela

An lakadawa ‘yan majalisar Venezuela duka

Manajan kamfanin na Atlas Security, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, mutane da dama sun nemi aiki a kamfanin wanda yawancinsu a matsayin masu gadi a gonakin da ke yammacin jihar Zulia.

Shugaban kasar Nicolas Maduro, ya ce kasar ta samu kanta cikin wannan yanayi ne saboda matakan karya tattalin azrikin da Amurka ta dauka a kanta ne.

An umurci Facebook ya daina bibiyar mutane


FacebookHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Facebook na bibiyar mutanen da ba su mu’amula da shi

Kotun Belgium ta bukaci kamfanin Facebook ya dakatar da bibiyar mutane ba tare da izininsu ba.

Kotun ta bukaci kamfanin ya share dukkanin bayanan da ya tattara a kan mutanen da ba su amfani da Facebook.

Kotun ta yanke hukunci cewa Facebook ya saba doka ta hanyar tattara bayanan mutane ba tare da saninsu ba.

Hukumar da ke kare hakkin sirrin mutane a Belgium ta ce shafin Facebook ya karya dokarta ta hanyar amfani da Cookies domin bibiyar wasu shafukan intanet.

Facebook zai fuskanci tarar kudi $311,000 a rana idan har bai bi umurnin kotun ba.

Facebook ya ce zai daukaka kara domin kalubalantar hukuncin.

Kotun ta ce ya zama wajibi Facebook ya dakatar da bibiyar mutane da kuma tatsar bayanan adadin da lokacin da mutanen ke amfani da intanet a Belgium.

Sannan dole Facebook ya yi watsi da dukkanin bayanan da ya tatsa ba bisa ka’ida ba.

Tun a 2015 ne aka zargi Facebook da bibiyar mutanen da suka ziyarci wasu shafukan intanet ko da kuwa ba mambobinsa ba ne.

Buhari ya gana da gwamnonin APC a Daura


Shugaban Najeriya Muhammadu BuhariHakkin mallakar hoto
Femi Adeshina

Image caption

Gwamnonin APC sun samu Buhari a Daura

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi wata ganawar sirri da gwamnonin jam’iyyarsa ta APC 18 a garin Daura jihar Katsina.

An yi ganawar tsakanin Buhari da gwamnonin a yau Juma’a, kamar yadda Femi Adeshina mai magana da yawun shugaban ya sanar tare da wallafa hotunan ganawar a shafin Facebook.

Sai dai kuma gwamnonin Yobe da Plateau da Ogun da Benue da Osun sun tura mataimakansu ne suka wakilce su a taron.

Wadanda suka halarci ganawar a Daura sun hada da shugaban kungiyar gwamnonin kuma gwamnan Zamfara Abdul’aziz Yari Abubakar da gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da na Jigawa Badaru Abubakar da na Kaduna Malam Nasir El Rufa’i.

Sauran sun hada da gwamnan Imo Rochas Okorocha da gwamnan Bauchi Abubakar Muhammed da na Borno Kashin Shettima da na Edo Godwin Obaseki da na Kogi Yahaya Bello da Abubakar Sani Bello na Niger da kuma gwamnan Nasarawa Tanko Al-Makura.

Jam’iyyar APC dai na fama da rigingimun cikin gida tun bayan da ta lashe zaben shekarar 2015.

Yanzu haka rikicin APC a jihar Kaduna na ci gaba da ruruwa bayan da wani bangare na jam’iyyar ya yi ikirarin bude sabon ofis tare da shelar dakatar da wasu shugabanni a Jam’iyyar.

Wannan kuma na zuwa bayan rikici tsakanin tsohon gwamnan jihar Kano Rabi’u Musa Kwankwaso da mutumin da ya gaje shi, Abdullahi Umar Ganduje.

Dalilin rikice-rikicen jam’iyyar a wasu jihohi ne a makon da ya gabata shugaba Buhari ya kafa kwamiti domin sasanta ‘ya’yan jami’yyar.

Tsohon gwamnan Legas Alhaji Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Buhari ya nada a matsayin shugaban kwamitin da zai yi kokarin ganawa da sasantawa tare da inganta zamantakewar ‘ya’yan jam’iyyar.

An sanya dokar ta baci a Ethiopia


habashaHakkin mallakar hoto
Reuters

Gwamnatin Ethiopia ta sanar da sanya dokar ta baci a kasar, kwana daya bayan da Firai Ministan kasar ya yi murabus.

Wata sanarwa da gidan talbijin na kasar ya fitar, ta ce matakin ya zama dole ne saboda a rage yawan zanga-zangar adawa da gwamnati da ake ta yi a kasar.

an kashe gomman mutane an kuma ji wa wasu dama raunuka yayin da aka yi wani yajin aiki don neman a saki fursunonin siyasa.

Wannan ne karo na biyu da gwamnati ke sanya dokar ta baci domin shawo kan wannan rikici.

An fara sanya sanarwar ne a shafin Facebook na gidan talbijin din kasar. Sai dai ba ta fadi ainihin tsawon lokacin da dokar ta bacin za ta dauka ba, ko kuma ka’idojinsa.

Wannan mataki dai na zuwa ne kwana daya bayan murabus din Firai Minista Hailemariam Desalegn, ya sanar da cewa ya yi murabus saboda rikicin da kasar ke fuskantar.

Sai dai ana sa ran majalisar dokoki za ta dawo daga hutun da take yi don amincewa da murabus din nasa, wanda tuni jam’iyyun hadaka da ke mulki suka amince da shi.

An shafe shekara uku kasar habasha na fama da zanga-zangar nuna adawa da gwamnati a yankuna daban-daban da suka hada da Oromia, wanda shi ne yanki mafi girma a kasar.

Daga cikin bukatunsu dai har da neman kawo manyan sauye-sauyen siyasa,da hakkin mallakar fili da sakin fursunonin siyasa.

A makon da ya gabata be, kasar ta saki daruruwan fursunonin siyasa da ‘yan jarida, amma duk da haka an ci gaba da zanga-zangar.

A watan Oktobar 2016, gwamnati ta sanar da sanya dokar ta baci da ya dauki tsawon wata 10 ana yi.

Ko gwamnatin Nigeria na son kara farashin man fetur?


layin maiHakkin mallakar hoto
Getty Images

Masu fashin baki sun fara tsokaci kan cewa da alama gwamnatin Najeriya na iya kara kudin litar man fetur a wani mataki na kawo karshen karancin man fetir din.

Kimanin wata uku ke nan ‘yan kasar na fama da dogayen layuka a gidajen mai, ba ya da tsadar man.

A ranar Alhamis ne dai gwamnan jihar Bauchi Muhammd A Abubakar, wanda ya yi wa manema labarai bayani a karshen taron majalisar tattalin arzikin kasar, ya ce majalisar ta umarci daya daga cikin kwamiocinta karkashin jagorancin gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dan Kwambo, da ya yi duba kan farashin man fetir a kasashe masu makwabtaka da kasar.

Sannan kuma sai ya bayar da shawara dangane da farashin da ya dace a rinka sayar da litar man a Najeriyar.

Daga cikin bayanin da gwamna M.A Abubakar ya yi wanda ya fi daukar hankalin ‘yan Najeriya shi ne inda yake fadin cewa daya daga cikin dalilan da suka janyo matsalar karancin man fetur din da ake fama a kasar taki ci taki cinyewa, ita ce yadda ‘yan wasu ‘yan kasuwa kan karkakatar da akalar man da aka ba su zuwa wasu kasashe masu makwabtaka saboda ya fi daraja a can.

Rahotanni dai na cewa Najeriya ce kasar da ake sayar da man fetur a farashi ma fi rahusa a Afirka.

Yadda masu sharhi ke kallon lamarin

Bala Zaka, Masanin harkar makamashi a jihar Legas da ke kudancin Najeriya

“Kara farashin ba zai taimaka a magance karancin man fetur ba. Ana rayuwar kunci yanzu a kasar da kuma tsanani. Idan dai har gwamnati ta ce za ta dauki matakin kara kudin (tatsattsen lu’u-lu’u) man fetur, to gaskiyar magana ita ce a karshe gwamnati za ta nakasar da tattalin arzikin kasar nan, kuma komai zai durkushe.

Idan za ta bi wasu hanyoyin gara ta bi amma ban da karin farashin mai. Idan ba haka za a jefa Najeriya a wani yanayi da a karshe kowa sai ya ce da ya sani.”

Ina mafita?

“Abun da ya kamata a yi shi ne a kara matatun man fetur, domin idan muka ga duba za mu ga cewa tun tsakanin shekarun 1965 zuwa 1989 a lokacin shugabannin da muke da su sun gina matatun mai hudu. Biyu a Fatakwal, daya a Kaduna, daya a Warrri.

“Amma tun daga 1990 zuwa 2018 ba a sake kara gina ko matatar mai daya ba. Daga lokacin zuwa yanzu abubuwa sun karu, kamar motoci da masana’antu.

“Abun da ya kamata ayi shi ne tun da akwai man a Najeriya, to a hako shi a naira, a tura shi matatu a naira, a tace shi a naira, a kuma sayar wa ‘yan Najeriya a naira, mu yi amfani da nairarmu.

“Wannan zai taimaka ya raba mu da duk abun da ake magana a kan kudin kasashen waje.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

An shafe wata uku ana wahalar man fetur a Najeria

To idan aka bi wadannan matakai gaskiya za mu iya farfo da arzikin Najeriya,” in ji Bala Zaka.

‘Gara a kara kudin man’

Wasu ‘yan kasar dai na ganin gara a ce an yi mai gaba daya wato a kara kudin man idan har man zai samu maimakon karin bayan ‘yan kasa sun gama jigata.

Sai dai ana ganin shugaba Buhari ne ba ya son yin karin, watakila saboda tausayin talaka ko kuma tsoron ka da a kalli gwamnatin da mai son kara kudin man fetir har karo biyu.

Gwamnain APC ce dai ta kara kudin man fetur jim kadan bayan hawanta, daga Naira 95 zuwa 145 ko wacce lita.

An ci zarafin bakaken fata a bikin sabuwar shekara ta China


chinaHakkin mallakar hoto
Youtube/CCTV

Wani wasan kwaikwayo da gidan talbijin na China ya nuna don murnar shiga sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar a ranar Alhamis, ya jawo ce-ceku-ce akan yadda aka nuna banbancin launin fata.

A wasan kwaikwayon, wanda aka shirya don nuna alakar ‘yan Afirka da China, sai aka sanya wata ‘yar yankin Asiya ta shafa shuni fuskarta da kuma manyan mazaunai.

Mutane da dama na daukar yin amfani da kayan kwalliyar da zai mayar da fuskar mutum baka, a matsayin cin fuska sosai.

Bikin sabuwar shekarar, wanda aka saba yi duk shekara ya shahara sosai, kuma kusan mutum miliyan 800 ne ke zuwa kallonsa.

Wasu masu sa ido sun nuna cewa hakan ba zai kasance cin fuska ga ‘yan Afirka ba.

Duk da haka, wannan ba shi ne karo na farko da wasannin nishaɗi na China suka haifar da rikici ba, ta yadda ake ganin suna nuna kabilanci da wariyar launin fata.

An fara bikin sabuwar shekarar ne da nuna wata kungiya ta masu raye-raye ‘yan Afirka, da kuma mutane da suka yi shiga kamar zakuna da bareyi da jakunan dawa.

Daga nan kuma sai aka gabatar da wasan kwaikwayo inda wata bakar mata ta umarci wani dan China da ya fito a matsayin mijinta ya durkusa a yayin da ya hadu da mahaifiyarta don gaishe ta.

Sai dai a yayin da yarinyar ta kasance baka ce, sai wacce ta fito a matsayin uwar tata ta kasance ‘yar China ce amma ta shafa bakin fenti a fuskarta, ta kuma sanya manyan mazaunai na karya, a matsayin tana kwaikwayar yadda halittar ‘yan Afirka take.

'Yan bindiga sun kashe akalla mutum 35 a jihar Zamfara


Wadansu mata bayan da aka kai wani hari a jihar Zamfara a shekarar 2013Hakkin mallakar hoto
AFP

Image caption

Wadansu mata bayan da aka kai wani hari a jihar Zamfara a shekarar 2013

Wadansu da ake zargi ‘yan bindiga ne sun kashe akalla mutum 35 wannan makon a jihar Zamfara da ke yankin arewa maso yammacin Najeriya.

Maharan sun kai harin ne a kan babura, inda suka tsare wata mota da ke dauke da wadansu ‘yan kasuwan jihar, kamar yadda shaidu suka bayyana.

Daga nan ne sai suka yanka makogwaro direban kafin suka fara bude wa motar wuta, abin da ya jawo mutuwar dukkan mutanen da ke cikin motar.

Bayan faruwar wannan ne, sai ‘yan bindigar suka tafi wata kasuwa suka fara harbi kan mai uwa da wabi, inda suka sake kashe wani mutum guda.

Zuwa yanzu dai, jami’an tsaro ba su bayyana adadin mutanen da suka rasa rayukansu ba sanadiyyar hare-haren wanda ake zargin barayin shanu da kai wa.

Jihar Zamfara ta sha fuskantar hare-hare daga mutanen da ake zargi barayin shanu ne a baya.

A watan Nuwambar bara, akalla mutum 24 ne suka rasa rayukansu kuma aka cinnawa gidajen jama’a da dama wuta a jihar.

Goron Ghana ya fi armashi a Nigeria


Mutanen Najeriya sun fi jin dadin goron GhanaHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Mutanen Najeriya sun fi jin dadin goron Ghana

Wani mai sayar da Goro a Najeriya, Danladi Mai Goro, ya ce goron da ake shigowa dashi daga kasar Ghana yafi armashi, ma’ana mutane sun fi son sa.

Mai sayar da goron ya shaida wa BBC cewa, yawanci goron kasar Ghana ake kawo wa Najeriya ana dasawa, kuma Ghana tafi Najeriya yawan goron ma.

Kasar Ghana dai na shigo da goro Najeriya kusan kashi uku, da suka hada da jan daushe da dan Ankara wanda shi fari ne, sannan kuma da wani goron wanda bai kai daushe tsada ba.

Duk da bukatar goron da ake a koda yashe, a yanzu haka farashinsa ya yi tashin gwauron zabi a kasuwannin Najeriya.

‘Yawan cin kayan marmari na iya kawo tsawon rai’

Ganduje ba zai iya ba mu wajen kiwo ba – Fulani makiyaya

Danladi mai goro ya ce, farashin goron na tashi ne saboda wani sa’in ya kan yadu sosai, yayin da wani lokaci kuma sai a samu akasin haka.

Ya ce a bana, gaskiya bai yi ‘ya ‘ya sosai ba, amma suna sa rai yanzu da alama ya dan fara toho sosai.

Danladi mai goro, ya ce suna sa rai nan da zuwa watanni hudu masu zuwa farashin goron zai yi sauki saboda zai wadata.

Akwai dai kasashe da dama da ke shigo da goro Najeriya baya ga Ghana, akwai Ivory Coast da kuma Saliyo.

An kama likitan bogi a jihar Nasarawa


Wasu daga cikin matan sun ce likitan ya karbi makudan kudade daga hannunsuHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Wasu daga cikin matan sun ce likitan ya karbi makudan kudade daga hannunsu

Hukumomi a Najeriya na shirin gurfanar da wani mai maganin gargajiya da ake zargi da safarar jarirai.

Hukumar yaki da safarar mutane ta kasar, Naptip ta damke Dr Akuchi ne a ‘yan makonnin da suka wuce bisa zarginsa da taimaka wa mata samun ciki na bogi daga bisani kuma ya basu jarirai.

Jami’an hukumar sun zargi likitan gargajiyan da yi wa mata 160 maganin samun ciki na bogi a tsawon shekaru hudu da ya yi yana wannan aiki a wani asibiti da ke jihar Nassarawa.

Wasu daga cikin matan sun shaidawa BBC cewa mutumin ya karbi makudan kudade daga hannunsu.

Hukumar ta NAPTIP ta ce nan bada jimawa ba zata gurafar da Dr Akuchi a gaban kotu.

Yankin kudu mo gabashin Nigeria dai ya yi kaurin suna wajan safarar jarirai, inda ko shekarar 2011 yan sanda suka kai samame a wani gida da ke Aba a jihar Abia inda suka gano yan mata fiye da 30 wadanda ake zargin ana yi mu su ciki domin su sayar da jariransu.

Kayanmu ba su da daraja a Turai — 'Yan kasuwa


Doya na daga cikin kayan abincin da ake fita da su kasashen waje domin sayarwa daga NajeriyaHakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Doya na daga cikin kayan abincin da ake fita da su kasashen waje domin sayarwa daga Najeriya

A Najeriya, mahukunta na wani sabon yunkuri na kyautata safarar kayan gona zuwa kasashen waje da nufin fadada kafofin samun kudin-shiga mai makon dogaro da mai.

To sai dai kuma wasu ‘yan kasuwa, sun ce duk wani kokari da za suyi don tallata kayan Najeriya zuwa kasashe ketare, da wuya ya yi tasiri.

‘Yan kasuwar dai na cewa suna cin karo da matsaloli a wannan harka, ciki har da karancin jari da rashin darajar kayan Najeriyar a kasuwannin kasashen Turai.

Alhaji Kamal Abdulkadir Mustapha, dan majalisar ‘yan kasuwar jihar Kano ne da ke arewacin Najeriya, wanda kuma ke fataucin kaya zuwa kasashen turai, ya shaida wa BBC cewa, kayansu na fuskantar kalubale sosai a kasashen waje, saboda yawanci ‘yan Najeriya sun yi suna wajen aika abubuwa wanda suke jabu, marassa nagarta, hakan ya sa idan ka kai kaya daga Najeriya ake fuskantar kalubale.

Alhaji Kamal, ya ce ” Wannan dalili ne ya sa wasu ‘yan kasuwar Najeriyar kan gwammace su kai kayansu Nijar ko Ghana ko kuma Cotonou, domin su auna kayansu su tura su ta can, don su samu biyan bukata wato ta yadda idan an kai su kasashen waje za a saye su daraja”.

Kasar UAE na shirin fara noma abinci a duniyar Mars

Zafi na haifar da karancin abinci mai gina jiki

A kan wadannan dalilai, ‘yan kasuwar suka ce dole ne sai gwamnati ta taimaka wajen kare martabar kayayyakin da suke samarwa a idon kasashen duniya, idan ana so kasuwancinsu ya bunkasa.

To yanzu dai, gwamnatin Najeriyar ta ce bisa la’akari da irin kalubalen da ‘yan kasuwar ke fuskanta, hakan ya sa hukumar bunkasa fataucin kayan Najeriya zuwa kasashen waje ta fito da wani shiri na kara wa ‘yan kasuwar kwarin gwiwa.

Hukumar dai ta na hada wasu fatake a wasu manyan biranen kasar domin wayar musu da kai a kan sabon shirinta game da bunkasa fitar da kayayyakin amfani gona zuwa kasashen waje.